Zaben 2027: An Bukaci Tinubu Ya Kori Ministoci 2 kan Wasu Zarge Zarge

Zaben 2027: An Bukaci Tinubu Ya Kori Ministoci 2 kan Wasu Zarge Zarge

  • Kungiyar APC League of Democrats ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi sauyi a majalisar ministocinsa domin kara inganci gabanin zabubbukan 2027
  • Ta yi nuni da cewa akwai ministoci biyu da ya kamata a kora, tana zarginsu da kawo cikas ga kokarin farfado da tattalin arzikin kasa da gwamnatin Tinubu ke yi
  • A cewarta, rashin daukar matakin da ya dace a kan lokaci na iya jefa damar APC a zaben 2027 cikin hadari ganin an fara shinshino shekarar shiga takara a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar APC League of democrats ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi garambawul a majalisar ministocinsa.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya kori wasu daga cikin ministocinsa bisa zargin lalata kokarin da gwamnatinsa ke yi.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

An bukaci Tinubu ya kori Ministoci biyu daga aiki
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron FEC Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar New Telegraph ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoranta na kasa, Babajide Oyewole, da sakatare, Cif Rowland Okonkwo, suka sanya wa hannu a ranar Litinin, 2 ga Fabrairun 2026.

Kungiya ta ba Shugaba Tinubu shawara

Kungiyar ta ce tuni ya kamata a sauya fasalin majalisar ministocin, inda ta bukaci a sallami wasu ministoci baki daya daga aiki.

Ta bukaci Shugaba Tinubu da kar ya kara jinkiri wajen aiwatar da “wannan muhimmin aiki na gaggawa”, tana mai gargadin cewa duk wani jinkiri zai kara jawo wa gwamnati illa tare da rage damar APC a babban zaben 2027.

"Mu gogaggun ’yan siyasa ne, kuma muna iya gane inda aka dosa idan masu mukami na aiki sabanin muradun gwamnati da shirye-shiryenta, alhali suna nuna kamar wakilanta ne."
“Ba wannan ne karo na farko ba. Mun taba ganin irin wannan a baya, kuma ba za mu bari tarihi ya sake maimaita kansa ba. Hakan ya faru a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan; wasu daga cikinmu sun hango matsalar tun wuri sun kuma daga murya, amma ba a dauki mataki ba."

Kara karanta wannan

Malami ya dauki mataki na hana EFCC kwace kadarori 57 da ya mallaka a Abuja, Kano

- Babajide Oyewole

Shawarar sallamar ministoci biyu

Kungiyar ta APC ta ambaci Ministan kudi, Wale Edun, da kuma karamar Ministar Kudi, Dr. Doris Uzoka-Anite, a matsayin wadanda ya kamata a sallame su nan take, shafin Politics Nigeria ya kawo labarin.

“Ministocin da ke aiki tukuru, irin su Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da Ministan ayyuka, Dave Umahi, za a iya barinsu a mukamansu."
"Amma yawancin sauran ministocin ya kamata a yi musu sauyi domin a samu inganci da kyakkyawan aiki.
“Dole ne a sallami Ministocin kudi guda biyu; Wale Edun da Doris Uzoka-Anite cikin gaggawa, domin amfanin jam’iyyarmu mai girma da kuma zaman lafiyar kasa.”

- Babajide Oyewole

Kungiyar ta zargi Edun da Doris Uzoka-Anite da kin bin umarnin Shugaba Tinubu wajen warware rikicin da ya dade yana gudana tsakanin gwamnatin tarayya da ’yan kwangilar cikin gida a Najeriya.

Kungiya ta ba Tinubu shawara kan wasu Ministocinsa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Damuwar 'ya 'yan APC kan zaben 2027

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi abin zai ba Tinubu damar cin zabe cikin sauki a 2027

Kungiyar ta kara da gargadin cewa idan ba a magance lamarin cikin lokaci ba, hakan na iya illata damar APC a zaben 2027.

"Ba za mu bari masu yi wa kasa zagon kasa su sake rubuta tarihin 2015 a zabubbukan da ke tafe ba. Dole ne shugaban kasa ya tashi tsaye ya amsa wannan kira na kishin kasa daga ’yan Najeriya, ya yi abin da ya dace tun kafin lokaci ya kure.”

- Babajide Oyewole

Hanyar cin zaben Tinubu cikin sauki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Bello Matawalle ya bayyana cikakken kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027.

Matawalle ya kara da cewa idan aka ba Shugaba Tinubu damar kammala shirye-shiryen da yake yi na gyara, babu shakka zai samu gagarumar nasara a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng