Muhimman Nade Naden da Gwamna Abba Ya Yi bayan Sauya Sheka zuwa APC
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya a hukumance.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abba Kabir Yusuf ya sauya shekar a ranar, 25 ga watan Janairun 2026 yayin wani gagarumin taro da aka shirya a gidan gwamnatin Kano.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro muhimman nade-naden da gwamnan ya yi bayan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC.
Wasu masu mukamai sun bar gwamnatin Abba
Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC ta jawo wasu daga cikin masu mukamai a gwamnatinsa sun ajiye aikinsu.
Ajiye mukaman nasu na da nasaba da kin yarda su bi Gwamna Abba zuwa jam'iyyar APC musamman saboda alakarsu da Rabiu Kwankwaso.
Daga cikin wadanda suka ajiye mukamai akwai kwamishononi da hadiman gwamnan, inda suka zabi su ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP.
Hakazalika, wasu shugabanni hukumomin gwamnatin jihar Kano, sun zabi su ajiye mukamansu a bisa dalilin sauya shekar da Gwamna Abba ya yi.
Gwamna Abba Gida Gida ya yi nade-nade
Sai dai, jim kadan bayan komawarsa APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da yin sababbin nade-nade a gwamnatinsa.
Sababbin nade-naden na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.
Gwamnan ya maye gurbin wasu daga cikin mukaman da masu rike da su, suka yi murabus bayan ya shiga jam'iyyar APC.
1. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji)
Daga cikin sababbin nade-naden da Gwamna Abba ya fara akwai na Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji), wanda aka nada a matsayin mai ba gwamna shawara ta musamman kan harkokin jin kai a ofishin gwamna.
Kafin samun wannan matsayi, Alhajiji ya rike mukamin babban mataimaki na musamman a gwamnatin Kano kuma da an fara zancen za a ba shi takarar majalisar dokoki.
2. Hajiya Aisha Tamburawa
Haka kuma, an nada Hajiya Aisha Tamburawa a matsayin Mai ba Gwamna shawara a kan yada kyawawan ayyukan gwamnati.
Kafin nadin nata, Hajiya Aisha ta kasance 'Supervisory Councillor' a Dawakin Tofa a Arewacin Kano.
3. Injiniya Mukhtar Yusuf
A bangaren ruwa, Injiniya Mukhtar Yusuf ya samu karin girma zuwa shugaban hukumar WRECA.
Injiniya Mukhtar Yusuf ya kasance mataimakin shugaban hukumar kafin a yi masa karin girma zuwa mukamin shugaba.
4. Zakari Usman Balan
Hakazalika, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba Zakari Usman Balan mukami a hukumar WRECA mai kula da samar da ruwan sha a Kano.
Gwamna Abba ya nada Zakari Balan Usman a matsayin mukamin mataimakin shugaba na hukumar WRECA.
5. Mukhtar Bello Maisudan
Sababbin nade-naden Gwamna Abba sun kai zuwa hukumar tallafin karatu ta jihar Kano bayan murabus din da tsohon shugaban hukumar ya yi.
Gwamna Abba ya nada malami daga jami'ar Bayero, Dakta Mukhtar Bello Maisudan a matsayin shugaban hukumar tallafin karatu ta jihar Kano.
6. Injiniya Abba Kankarofi
Injiniya Abba Kankarofi ya samu karin girma zuwa shugaban hukumar kula da tituna da gyare-gyare ta Kano (KARMA).
Bayanan da aka samu daga shafin yanar gizon gwamnati ya ce Abba ya yi masa karin girma ne daga matsayin mukamin mataimakin shugaban hukumar KARMA.
7. Musayyib Kawu Ungogo
Hon. Musayyib Kawu Ungoggo ya zama Shugaban hukumar adana namun dawa na jihar Kano bayan an fara taya shi murnar samun takarar majalisar dokoki.
Kafin samun wannan matsayi ya taba rike mukaman siyasa daban-daban ciki har da na Kansila. Matashin yana cikin 'yan siyasa masu tasowa a Ungogo.
8. Abubakar Ibrahim Matawalle
A ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026, Gwamna Abba ya sanar da nadin Abubakar Ibrahim Matawalle a matsayin mukaddashin shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano.
Abubakar Ibrahim Matawalle ya taba rike irin wannan mukami a baya kafin ya yi ritaya daga aikin gwamnati.

Source: Facebook
9. Barista Rahama Malam Alhaji
Gwamna Abba ya nada Barista Rahama Malam Alhaji a matsayin shugabar cibiyar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Barrista Rahama Malam Alhaji kwararriyar lauya ce mai gogewa sama da shekaru bakwai, musamman a fannonin shari’a, dokokin kamfanoni, dokokin lantarki, bin ka’idoji, da warware rikice-rikice.

Kara karanta wannan
Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano
10. Aina’u Ade
An kara wa Ainau Ade girma daga Mataimakiya ta musamman zuwa babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin Kannywood.
Sanarwar ta bayyana cewa karin girman na ta ya biyo bayan kyakkyawan aikinta da jajircewarta a mukamin da ta rike a baya.
Gwamna Abba ya fadi Sarkin Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba gardama kan batun masarautar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Muhammadu Sanusi II ne zai ci gaba da rike sarautar masarautar Kano.
Ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa akwai yiwuwar a sauke Sanusi II domin dawo da Sarki Aminu Ado Bayero a kan kujerar sarauta.
Asali: Legit.ng


