Tofa: Gwamna Ya Rufe Dukkan Makarantu, Ya Sanya Dokar Zaman Gida Ta Awanni 20

Tofa: Gwamna Ya Rufe Dukkan Makarantu, Ya Sanya Dokar Zaman Gida Ta Awanni 20

  • Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya rufe dukkan makarantu a yankin Amasiri tare da sanya dokar hana fita na awanni 20 bayan mummunan hari
  • Rahoto ya ce harin ya yi sanadin kisan mutane hudu da yanke musu kai, tare da kona gidaje sama da tara a kauyen Okporojo
  • Gwamnatin Ebonyi ta tube sarakunan gargajiya biyu tare da rushe dukkan shugabancin al’umma a Amasiri domin dawo da doka da oda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abakaliki, Ebonyi - Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantu a wasu yankuna a jihar.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne a yankin Amasiri da ke Karamar Hukumar Afikpo, tare da sanya dokar hana fita ta awanni 20 a kullum.

Gwamna ya rufe makarantu a jiharsa
Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi. Hoto: Hon. Francis Nwifuru.
Source: Facebook

Dalilin daukar matakan a Ebonyi

Da yake zantawa da ’yan jarida bayan taron majalisar tsaro a Abakaliki, gwamnan ya bayyana jerin matakan tsaro da na gudanarwa domin dawo da zaman lafiya da hana sake faruwar irin wannan hari, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ba rufa rufa: Sunayen mutum 40 da aka kama bisa shirin yi wa Tinubu juyin mulki

Matakin ya biyo bayan wani mummunan hari da aka kai a kauyen Okporojo, da ke cikin yankin Oso Edda a Karamar Hukumar Edda, wanda ake zargin wasu ’yan ta’adda daga Amasiri ne suka kai harin.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya yi sanadin kisan mutane hudu tare da yanke musu kai, yayin da aka kona gidaje fiye da tara a yankin.

An yanke wadannan matakai ne bayan taron gaggawa da Majalisar Tsaron Jihar Ebonyi ta gudanar a daren ranar Asabar, domin daukar matakan da za su kawo karshen tashin hankalin.

Tun da farko a ranar Asabar, Gwamna Nwifuru ya ziyarci yankin da abin ya shafa, inda ya jajanta wa mazauna yankin, tare da umartar jami’an tsaro da su kama tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu a harin.

Nwifuru ya kara da cewa majalisar ta bayar da umarnin rushe dukkan tsarin shugabancin al’umma a yankin, ciki har da shugabannin kungiyoyin ci gaba, hakimai, shugabannin mata da na matasa, tare da duk wata kungiya ta hukuma ko ba ta hukuma ba.

Tashin hankali ya yi sanadin sanya dokar hana fita
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Umarnin da Gwamna ya bayar a Ebonyi

Gwamnan ya ce an umarci shugabannin kananan hukumomin Afikpo, Ivo, Ohaozara da Onicha da su karbi ragamar tafiyar da harkokin mulki a Amasiri har zuwa wani lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya tube rawanin sarki, ya kori wasu jami'an gwamnati daga aiki

“Gwamnati ta amince da shawarar majalisar, ta rushe dukkan shugabannin kungiyoyin ci gaba, hakiman kauyuka, shugabannin mata da na matasa, kungiyoyin matasa, mata da sauran kungiyoyi a Amasiri.”

Ya kara da cewa an bayar da umarnin rufe dukkan cibiyoyin gwamnati a yankin, ciki har da makarantu masu zaman kansu da na gwamnati, da kuma Cibiyar Ci gaban Amasiri.

Nwifuru ya ce an shirya kudurin doka da za a mika wa Majalisar Dokokin Jihar Ebonyi domin soke dokar da ta kafa Cibiyar Ci gaban Amasiri.

A cewarsa:

“Daga gobe da safe, ba za a sake yin karatu a Amasiri ba, kuma ba za a sake samun cibiyar ci gaba a yankin ba.”

Gwamnan ya kara da cewa an sanya dokar hana fita a Amasiri daga karfe 2:00 na rana zuwa karfe 10:00 na safe a kowace rana.

A karkashin dokar, dukkan kasuwanni, shaguna, bankuna, wuraren kasuwanci, ma’adinan dutse da sauran harkokin kasuwanci za su kasance a rufe a lokutan da aka kayyade.

Gwamna ya tube Sarki, ya kori mukarrabansa

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Francis Nwifuru ya fusata matuka kan mummunan farmakin da aka kai kauyen Okporojo, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane hudu.

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

Rahotanni sun nuna cewa mutanen garin Amasiri ne suka kai harin, saboda rikicin da ke tsakaninsu da kauyen Okporojo.

Gwamna Nwifuru ya tsige sarkin yankin tare da korar duk wani dan garin Amasiri da ke rike da mukami a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com