‘Ba Talauci ba ne,’ Peter Obi Ya Fadi Ainihin Matsalar da Ke Addabar Najeriya

‘Ba Talauci ba ne,’ Peter Obi Ya Fadi Ainihin Matsalar da Ke Addabar Najeriya

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fadi musabbabin matsalolin Najeriya sabanin yadda wasu ke yadawa
  • Tsohon gwamnan Anambra ya bukaci ’yan Najeriya su rika yi wa ’yan siyasa addu’a domin Allah ya shiryar da su amfani da kudin jama’a da gaskiya
  • Obi ya yaba wa Gwamna Seyi Makinde, yana mai cewa Ibadan ta samu ci gaba sosai, tare da fatan Oyo za ta fi bunƙasa a shekaru 50 masu zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa tushen matsalolin Najeriya na hannun ’yan siyasa ne, ba wai talauci ba.

Peter Obi ya soki yan siyasa, yana mai cewa shugabannin kasar sun kasa tafiyar da dimbin albarkatun da Allah ya albarkaci Najeriya da su.

Kara karanta wannan

Bayan jirgi marar matuki ya hallaka sojoji, rundunar ta fadi matakin da ta dauka

Obi ya fadi tushen matsalolin Najeriya
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

Obi ya roki yan Najeriya addu'a

Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin wani taron godiya da aka shirya domin cika shekaru 50 da kafuwar Jihar Oyo, wanda aka gudanar a Cocin St Peter’s Cathedral da ke Aremo, Ibadan, cewar Vanguard.

A jawabinsa, Obi ya roki ’yan Najeriya da su rika yi wa ’yan siyasa addu’a, domin Allah ya shiryar da zukatansu wajen amfani da kudaden jama’a ta hanyar da za ta amfanar da kowa.

Ya ce:

“Ina da roko ga ’yan Najeriya. Don Allah ku tuna da mu ’yan siyasa a addu’o’inku. Mu ne matsalar Najeriya. Najeriya ba kasa ce matalauciya ba, illa dai an yi mata mulki mara kyau.
"Ku tuna da mu a addu’a, Allah ya taba zukatanmu mu rika amfani da kudin jama’a domin alherin jama’a. Idan muka yi haka, Najeriya za ta gyaru.”
Peter Obi ya bukaci addu'o'i ga Najeriya
Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Addu'ar da Peter Obi ya yi ga Najeriya

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma yi addu’ar Allah ya albarkaci ’yan Najeriya da iyalansu baki daya.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya kawar da NNPP, ya faɗi jam'iyyar da za ta kayar da Tinubu a 2027

Haka kuma, Obi ya yi tsokaci kan cigaban da aka samu a birnin Ibadan karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, yana mai bayyana birnin a matsayin mai tarihi da sauyi.

Ya ce Ibadan gari ne mai dimbin tarihi, inda yawancin ’yan Najeriya suka samu asalin tarbiyyarsu tun shekaru masu yawa da suka gabata.

“Ko da yaushe abin alfahari ne a gare ni in kasance a Ibadan. Na zo nan ranar Talata domin ziyartar jami’a, Ibadan birni ne na ilimi, birni ne na ci gaba.”

- In ji Obi

Obi ya ce Ibadan ta samu gagarumin ci gaba a karkashin gwamnatin Gwamna Seyi Makinde.

Ya kuma bayyana fatan cewa shekaru 50 masu zuwa na Jihar Oyo za su kasance abin koyi ga sauran jihohi, cewar The Guardian.

Neman takara ka iya sa Obi ya bar ADC

Kun ji cewa ana ci gaba da tattaunawa da muhawara kan wanda zai iya samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar hadaka ta ADC.

Masana harkokin siyasa dai na ganin fafatawar ta fi zafi ne tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Peter.

Wani mai sharhi kan al'amuran jama'a ya bayyana cewa akwai yiwuwar Peter Obi ya tattara kayansa ya fice daga ADC kafin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com