Dokar Zabe ta 2026: Majalisa ta Shirya Zaman Yiwa Duba Lam'a a Dokar Zaben Najeriya

Dokar Zabe ta 2026: Majalisa ta Shirya Zaman Yiwa Duba Lam'a a Dokar Zaben Najeriya

  • Majalisar Dattawa a Najeriya ta bayyana shirya zaman gaggawa a ranar Talata domin tattauna batutuwan dokar zabe
  • Wannan na zuwa ne bayan da ake tada jijiyar wuya kan wasu sassa na dokar da wasu ke ganin ya kamata majalisar ta duba
  • Ba wannan ne karon farko ba da ake samun tangarda wajen aikin doka a Najeriya, an yi hakan a lokacin gyara dokar haraji ta kasa

FCT, Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta tsara zaman gaggawa na taron majalisa a ranar Talata, 10 ga Fabrairu, 2026, yayin da ’yan majalisa ke fuskantar matsin lamba daga jama’a da cece-kuce kan gyare-gyaren Dokar Zabe.

Sanarwar ta fito ne a ranar Lahadi cikin wata takarda da Magatakardar Majalisar Dattawa, Emmanuel Odo, ya sanya wa hannu, yana isar da umarni daga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Za a fara wannan zama na musamman da karfe 12:00 na rana a zauren Majalisar Dattawa, kuma an bukaci dukkan sanatoci su halarta, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Majalisa ta shirya zama kan dokar zabe
Shugaban majalisa da yadda ake zaman majalisa a Najeriya | Hoto: SenateNGR
Source: Twitter

Dalilin zaman gaggawan

Duk da cewa sanarwar ba ta fayyace ajandar taron ba, lokacin da aka tsara zaman ya zo ne kwanaki kadan bayan Majalisar Dattawa ta kammala tattaunawa kan Kudirin Gyaran Dokar Zabe.

Hankalin jama’a ya karkata sosai kan kin amincewa da wani muhimmin sashe na kudirin da zai tilasta a rika tura sakamakon zabe ta na’ura kai tsaye daga rumfunan zabe.

A maimakon haka, Majalisar Dattawa ta bar tsarin da ke ba da damar tura sakamakon ta na’ura ne kawai bayan an kammala kirga kuri’u kuma an sanar da su a bainar jama’a a rumfunan zabe.

Masu suka na cewa wannan mataki ya raunana kokarin tabbatar da gaskiya da kungiyoyin fararen hula da masu fafutukar gyaran tsarin zabe ke nema.

Tashin hankalin jama’a da matsin siyasa

Tun bayan wannan hukunci na Majalisar Dattawa, an samu suka masu yawa daga kungiyoyin fararen hula, masu fafutuka, kungiyoyin kwadago da ’yan adawa.

Kara karanta wannan

Rasuwar sanata ta girgiza Majalisar Dattawa, ta yi zama na musamman don girmama shi

Mutane da dama na ganin kin tilasta tura sakamakon zabe ta na’ura a matsayin koma baya ga yunkurin tabbatar da sahihin zabe, musamman bayan rigingimun da suka biyo bayan babban zaben 2023.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi barazanar shirya zanga-zangar kasa baki daya, har ma da yiwuwar kauracewa zaben 2027, matukar ba a fayyace ko za a saka tura sakamakon ta na’ura a cikin dokar ba.

Kungiyar ta ce yadda Majalisar Dattawa ta tafiyar da batun gyaran dokar ya rikita jama’a, kuma hakan na iya kara raunana amincewar al’umma ga tsarin zabe.

Matsayar shugabancin Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, tare da wasu sanatoci, sun kare matakin da majalisar ta dauka, suna jaddada cewa tura sakamakon zabe ta na’ura har yanzu yana cikin doka.

Sun ce damuwar da aka nuna kan rashin ingancin kayan aiki da kuma yiwuwar rikice-rikicen shari’a ne suka sa aka yanke wannan shawara.

Akpabio ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ba za ta bari matsin lamba daga waje ya tsoratar da ita ba wajen aiwatar da nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.

Kara karanta wannan

An samu sabani tsakanin Majalisar Dattawa da ta wakilai wajen gyara dokar zaben Najeriya

Abin da ake tsammani a zaman Talata

Yayin da fata da tsammanin jama’a ke karuwa, zaman gaggawar ranar Talata na iya sa Majalisar Dattawa ta sake duba sashe-sashen da ake takaddama a kansu na Kudirin Gyaran Dokar Zabe.

Masana shari’a sun nuna cewa majalisar na iya yin gyara ko karin bayani domin magance damuwar da ake da ita kan gaskiya da kuma kwantar da hankalin jama’a.

Haka kuma, yiwuwar kalubalen shari’a da zanga-zangar jama’a na iya yin tasiri kan yadda zaman zai gudana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng