Karshen Alewa: Sojojin Najeriya Sun Kashe Abu Khalid, Babban Jagoran Ƴan Ta'adda

Karshen Alewa: Sojojin Najeriya Sun Kashe Abu Khalid, Babban Jagoran Ƴan Ta'adda

  • Dakarun sojin Najeriya sun kashe Abu Khalid, mataimakin babban kwamandan Boko Haram, tare da mayaka 10 a wani harin dare da suka kai Sambisa
  • Rundunar Operation Hadin Kai ta gano manyan makamai da kayan abinci da magunguna bayan fatattakar 'yan ta'addan a yankin karamar hukumar Konduga
  • Wannan nasara ta biyo bayan kashe wani fitaccen kwamandan ISWAP mai suna Julaibib wanda sojoji suka yi a cikin 24 da suka gabata a Damboa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Dakarun hadin gwiwa na rundunar Operation Hadin Kai sun samu gagarumar nasara ta hanyar kashe wani babban jagoran kungiyar Boko Haram.

An ce an kashe hatsabibin dan ta'addar wanda aka bayyana a matsayin mataimakin kwamandan Boko Haram, tare da wasu mayaka 10 a cikin dajin Sambisa dake Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara, an kashe babban kwamandan ISWAP

Sojojin Najeriya sun kashe wani babban kwamandan Boko Haram
Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a Arewa. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An hallaka babban kwamandan Boko Haram

Jami'in yada labarai na rundunar, Lt. Col. Sanni Uba ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar sojoji na X a ranar 1 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar ta ce an gudanar da wannan samame ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Asabar a yankin Komala dake karkashin karamar hukumar Konduga.

A yayin wannan samame, an ce dakarun sojojin kasa da taimakon dakarun sa-kai na CJTF suka far wa sansanin 'yan ta'addan ba tare da wani bata lokaci ba.

An kwato makamai daga 'yan ta'adda

Jami'in yada labarai na rundunar, Lt. Col. Sanni Uba, ya tabbatar da cewa Abu Khalid babban jagora ne a cikin tafiyar 'yan ta'addan, domin shi ne ke kula da dukkan dabarun yaki da tsare-tsaren yadda ake samar da kayan aiki da abinci a fadin yankin Sambisa.

Saboda haka, cire shi daga sahun rayayyu babban koma-baya ne ga ayyukan ta'addanci dake addabar mazauna yankin da ma shiyyar Arewa maso Gabas baki daya.

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

Bayan kammala fafatawar, dakarun sojin sun samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar, harsasai, kekuna masu yawa, da kuma maƙudan kayan abinci da magunguna wadanda 'yan ta'addan ke amfani da su wajen gudanar da rayuwarsu a cikin daji.

Rundunar ta bayyana cewa babu soja ko daya da ya rasa ransa ko ya samu rauni a wannan fafatawa mai zafi, kuma hakan ya kara wa dakarun kwarin gwiwa matuka.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce za ta ci gaba da tsage damtse wajen murkushe 'yan ta'adda.
Wasu sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji za su kara kakkabe 'yan ta'adda

Babban kwamandan rundunar ya jinjina wa dakarun bisa jajircewa da sadaukarwar da suke nuna wa wajen kare kasa, in ji rahoton Punch.

Ya kuma sake jaddada kudurin rundunar na ci gaba da kai hare-hare har sai an tabbatar da cewa dukkanin miyagu sun mika wuya ko kuma an gama da su baki daya.

Wannan nasara tana matsayin wani babban mataki na maido da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a yankunan da suka shafe shekaru suna fama da hare-haren 'yan bindiga da 'yan tada kayar baya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ware jiha 1 a Arewa da take so jami'an tsaro su kai jerin hare hare

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

Tun da fari, mun ruwaito cewa, dakarun sojojojin Najeriya sun sanar da nasarar kashe wani fitaccen kwamandan ISWAP mai suna Julaibib a yankin Gujba dake Timbuktu Triangle.

Sojojin sun samu nasarar hallaka tantirin kwamandan kungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP baya an gwabza fada a karamar hukumar Damboa, da ke jihar Borno.

Karin bayanan sirri sun kuma nuna cewa kawar da wannan jagoran ’yan ta’adda ya jefa ’yan ISWAP a yankin cikin rudani, inda aka kashe mayaka da dama a yayin wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com