Juyin Mulki: Ministan Tsaro Ya Faɗi Hukuncin da Ke Jiran Sojojin, Ya Yi Albishir ga Iyalansu

Juyin Mulki: Ministan Tsaro Ya Faɗi Hukuncin da Ke Jiran Sojojin, Ya Yi Albishir ga Iyalansu

  • Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi magana game da zargin wasu sojoji a yunkurin juyin mulki
  • Musa ya ce jami’an sojojin da aka kama kan yunkurin juyin mulki sun san illar abin da suka aikata da hukuncin da zai biyo baya
  • Sojoji sun tabbatar da cewa an gano shirin tun watan Satumba 2025, wanda ya hada da kashe Shugaba Tinubu, Shettima da tsare manyan jami’an soja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa ya bayyana damuwa game da yunkurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi.

Musa ya ce jami’an sojoji da aka kama kan yunkurin juyin mulki sun riga sun shirya fuskantar sakamakon aikinsu.

Hukuncin da ke jiran sojoji da ake zargi da yunkurin juyin mulki
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: HQ Nigerian Army, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Da yake magana a gidan talabijin na TRT World da aka wallafa a YouTube, Musa ya tabbatar da cewa za a bai wa wadanda ake zargi damar lauya da shari’a adalci.

Kara karanta wannan

Ba rufa rufa: Sunayen mutum 40 da aka kama bisa shirin yi wa Tinubu juyin mulki

Sojoji da aka kama kan zargin juyin mulki

An kama jami’ai 16 da ake zargi, ciki har da birgediya janar da kanal, a watan Oktoba 2025 bisa zargin karya dokokin aiki da rashin ladabi.

A ranar 26 ga Janairu, hedkwatar tsaro ta tabbatar da cewa lallai akwai shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sojoji sun ce an gano shirin ne ta hanyar hadin gwiwar leken asiri daga rundunar soji, DSS da hukumar leken asirin tsaro ta DIA.

Tinubu da wadanda aka yi niyyar kashewa

Rahoton ya nuna cewa shirin ya hada da yunkurin kashe Shugaba Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima da wasu manyan jami’an gwamnati.

Haka kuma, ana zargin masu shirin sun kuduri aniyar kama manyan shugabannin sojoji domin karbe iko a kasar.

Lamarin ya ta da maganganu musamman bayan rundunar sojojin ta musanta labarin cewa ana shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Alkawarin da Musa ya yi ga iyalan sojojin

Kara karanta wannan

Abin da aka tanadar wa iyalan sojojin da suka yi yunkurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki

Ministan ya ce gwamnati ba za ta bar iyalan wadanda ake zargi cikin wahala ba, duk da girman laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Ya ce:

“Sun san abin da zai biyo baya tun kafin su yanke shawarar yin haka, kuma dole sun yi tunanin iyalansu.”

Musa ya kara da cewa gwamnati tana tabbatar da cewa matan da ‘ya’yan wadanda ake zargi suna samun kulawa yadda ya kamata.

“Ba a bar iyalansu su shiga damuwa ba, gwamnati tana daukar nauyin rayuwarsu a wannan lokaci.”

Christopher Musa

A cewarsa, masu wannan yunkuri sun san hukuncin abin da suka aikata, kuma suna shirin fuskantar fushin doka da adalci.

Motoci, makamai da aka kama game da juyin mulki

Mun ba ku labarin cewa bayanai sun bankado makamai, motoci da kudade da aka kwato daga jami’an soja da fararen hula da ake zargi da shirya juyin mulki.

Bincike ya gano shirin wani makirci, inda aka tanadi manyan makamai, motocin aiki, da shirye-shiryen kashe manyan shugabanni.

Akalla jami’an soja 25 da wasu fararen hula za su fuskanci shari’a, yayin da ake zargin tsohon gwamna Timipre Sylva da hannu a batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.