Ba Rufa Rufa: Sunayen Mutum 40 da aka Kama Bisa Shirin yi wa Tinubu Juyin Mulki
- Hukumomin tsaro sun kammala bincike kan zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda aka gano mutane 40 da ake zargi da hannu
- Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wadanda aka tsare akwai manyan jami’an soji daga rundunoni daban-daban, jami’in ’yan sanda da kuma fararen hula.
- Bayanan da aka fitar sun bayyana cewa binciken ya bankado matakan leken asiri da aka dauka, daukar nauyi da kuma yada farfaganda a shirin juyin mulkin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce sun kammala bincike kan zargin shirin juyin mulki da nufin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ya sake tayar da muhawara kan tsaron dimokuradiyya a kasar.
Binciken, wanda aka gudanar ta hadin gwiwar rundunar sojin kasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta SSS, ya gano mutane 40 da ake zargi da shiga cikin shirin a matakai daban-daban.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa an fara cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin tun watan Oktoba, 2025, bayan samun bayanan sirri da ke nuna yiwuwar shirye-shiryen kifar da gwamnati ta karfi.
Sunayen wadanda aka kama:
1. MA Sadiq – Birgediya Janar – Hedikwatar Rundunar Sojoji
2. MA Ma’aji – Kanal – Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Tsaro
3. S. Bappah – Laftanar Kanal
4. AA Hayatu – Laftanar Kanal – Bataliya ta 130, Ogoja, Jihar Cross River
5. P. Dangnap – Laftanar Kanal – Bataliya ta Musamman ta 134
6. M. Almakura – Laftanar Kanal – Bataliya ta Musamman ta 197
7. AA Jarma – Laftanar Kanal – Kwamandan Bataliya ta 35, Katsina
8. SM Gana – Laftanar Kanal – Bataliya ta Rundunar Aiki ta 115
9. AD Dauda – Manjo – (ba a fayyace sashen aiki ba)
10. JM Ganaks – Manjo – Kwalejin Koyon Jagoranci da Tsare-tsare ta Rundunar Soji, Jaji
11. AJ Ibrahim – Manjo – Sashen Manufofi da Tsare-tsare, Hedikwatar Rundunar Sojoji
12. MM Jiddah – Manjo – Bataliya ta 26
13. MA Usman – Manjo – Bataliya ta 35
14. D. Yusuf – Manjo – Sansanin Aiki na Gaba Molai, Hedikwatar Sojoji
15. J. Iliyasu – Manjo – Garrison na Rundunar Soji ta 3
16. A. Mohammed – Manjo – Garrison na Birgediya ta 63
17. DB Abdullahi – Laftanar – Hedikwatar Rundunar Sojin Ruwa, Abuja
18. SB Adamu – Kwamandan Squadron – Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC)
19. NG Zuzu – Kwamandan Squadron – (ba a fayyace wurin aiki ba)
20. G. Binuga – Kyaftin – Birgediya ta 1 NMF
21. AA Yusuf – Kyaftin – Makarantar Kudi da Gudanarwa ta Rundunar Soji (NASFA)
22. I. Bello – Kyaftin – Garrison na Rundunar Soji ta 82
23. SS Felix – Laftanar – Rukunin ’Yan Sandan Soja na Rundunar Soji ta 81
24. J. Aminu – Laftanar – Hedikwatar Sashen Hulda da Jama’a na Rundunar Soji (DAPR)
25. Nasiru Ibrahim – Warrant Officer – Garrison na Rundunar Soji ta 82
26. Sanda Usman – Sajan – Bataliya ta Musamman ta 167
27. Mohammed Zubairu – Sajan – Bataliya ta Tsaron Fadar Shugaban Kasa ta 177
28. Momoh Audu – Kafral – Rundunar Artileri ta 343
29. Ahmed Ibrahim – Sufeto – Rundunar ’Yan Sanda
30. EO Victor – Kyaftin na Ruwa (mai ritaya) – Port Harcourt, Jihar Rivers
31. Umoru Zekeri – Ma’aikacin wutar lantarki – Kamfanin Julius Berger (Villa)
32. Y. Nasiru – Laance Kafral – Garrison na Rundunar Soji ta 82
33. Sambo Danladi – Laance Kafral – Garrison na Rundunar Soji ta 82
34. Abdul Abdullahi – Babban Sajan – Garrison na Rundunar Soji ta 82
35. Ali Isah – Direban motar asibiti – Villa
36. ML Mohammed – Kyaftin – Bataliya ta 18
37. UI Yusuf – Kwamandan Wing – Makarantar tuka jirgin sama, Enugu
38. IM Gana – Manjo Janar (mai ritaya) – Gidan Sojoji No. 34A, Kubwa, Abuja

Kara karanta wannan
Birgediya Janar Sadiq: Bayanan da muka sani kan sojan da ake zargi da hannu a 'juyin mulki'
39. Stanley Kingsley Amandi – Dan fim
40. Goni Bukar – (ba a fayyace aikinsa ba)

Source: Facebook
Iyalan sojoji sun roki Bola Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa iyalan wasu daga cikin sojojin da aka kama bisa zargin yukurin juyin mulki sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu.
A tattaunawa da aka yi da wasu daga cikinsu, sun roki shugaban kasar ya yi musu sassauci yayin da ake shirin mika su gaban alkali.
Rundunar tsaro ta bayyana cewa bayan kammala bincike za ta mika su kotu domin yanke musu hukunci, lamarin da ake ganin zai kai ga hukuncin kisa.
Asali: Legit.ng


