An Dura kan CAN da Ta Kare Shugaban INEC bayan Fada wa Amurka Ana 'Kashe' Kiristoci

An Dura kan CAN da Ta Kare Shugaban INEC bayan Fada wa Amurka Ana 'Kashe' Kiristoci

  • Kungiyar MURIC ta yi martani mai zafi kan kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Arewa game shugabancin INEC
  • MURIC ta caccaki kungiyar bisa kare Shugaban INEC, Joash Amupitan, kan zargin hannu wajen bata sunan Najeriya a waje
  • Kungiyar ta ce CAN ta kauce wa muhimmin batu, ta fi maida hankali kan zargin siyasantar addini maimakon amsa tambayar ko Amupitan ya rubuta takardar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmi, Muslim Rights Concern (MURIC), ta soki reshen Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) na Arewa.

Kungiyar ta caccaki CAN kan kare Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan da aka taso a gaba sai ya bar kujerar hukumar.

MURIC ta dura kan CAN game da shugabancin INEC
Shugaban INEC, Joash Amupitan yayin karbar rantsuwar kama aiki daga Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

MURIC ta shiga maganar kujerar shugaban INEC

Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan zartarwa na MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na kungiyar.

Kara karanta wannan

Malaman Kiristoci sun yi magana da murya 1 kan sauke shugaban INEC

Akintol ya ce kungiyar CAN ta yi watsi da muhimmin batu tana bin abin da bai dace ba wanda ke tabbatar da rashin adalci.

MURIC ta zargi CAN da kare Amupitan duk da ikirarin cewa yana da hannu wajen saka Najeriya cikin jerin kasashen da Amurka ke dauka a matsayin abin damuwa.

Kungiyar ta ce shugabannin CAN na Arewa sun fi karkata ga motsin rai maimakon fuskantar zargin da aka yi wa shugaban hukumar zabe kai tsaye.

Sanarwar ta ambato shugabannin CAN na Arewa, Reverend Joseph Hayab da Bishop Mohammed Naga, suna zargin Majalisar Shari’a ta Najeriya da siyasantar addini.

Wannan zargi ya biyo bayan bukatar da Majalisar Shari’a ta yi na a sauke Amupitan daga mukaminsa bisa zargin rubuta wata takardar shari’a.

MURIC ta caccaki CAN Arewa kan shugabancin INEC
Shugaban kungiyar MURIC, Ishaq Akintola. Hoto: MURIC.
Source: Twitter

MURIC ta zargi CAN da rashin adalci

MURIC ta ce kungiyoyi masu kishin kasa sukan fuskanci matsala kai tsaye, su ware gaskiya daga motsin zuciya ba tare da kauce wa tambayoyi ba.

Ta bayyana cewa CAN ta bar mai laifi ta maida hankali wajen kai hari ga wanda ya tona matsalar, abin da ta ce bai dace ba kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Maganar cire shugaban INEC ta girma, CAN ta ƙalubalanci majalisar shari'ar Musulunci

Kungiyar ta kwatanta lamarin da jarrabawa inda aka bar dalibin da ya yi magudi, aka hukunta mai kula da jarrabawar da ya bi ka’ida.

MURIC ta tambayi yadda CAN za ta watsar da batun kai rahoto kan Najeriya zuwa Amurka, ta fi mayar da hankali kan masu tambayar rahoton.

Ta ce abin mamaki ne CAN ta guji tabbatarwa ko karyata zargin cewa Amupitan ne ya rubuta takardar doka da ake magana a kai.

A cewar MURIC, CAN ta kauce wa batu, tana rawar gani da jan hankali maimakon bayar da amsa kai tsaye ga zargin da ake yi.

Kiristoci sun magantu kan kujerar INEC

Mun ba ku labarin cewa batun kiran a sauke shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.

Wata kungiya ta malalmai Kiristoci ta yi watsi da bukatar a sauke Farfesa Amupitan daga shugabancin hukumar zabe ta INEC.

Kungiyar ta jero wasu matsalolin da za su iya faruwa idan Shugaba Bola Tinubu ya sauke Farfesan daga kan mukamin da yake kai Read

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.