Abin da Aka Tanadar Wa Iyalan Sojojin da Suka Yi Yunkurin Yi Wa Shugaba Tinubu Juyin Mulki
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta kula da walwalar Iyalan sojojin da ake zargi da hannu a yunkurin yi wa Shugaba Bola Tinubu juyin mulki
- Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi bayan tabbatar da yunkurin juyin mulki
- Ya ce ya kamata a ce sojojin sun tuna da iyalansu kafin su kulla wannan makarkashiya amma duk da haka gwamnati ba za ta yi watsi da iyalansu ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta yi watsi da iyalan sojojin da ake zargi da kitsa juyin mulki ba.
Janar Musa ya ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa iyalan jami'an da ake zargi da hannu a yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu adalci.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Ministan tsaro ya faɗi hukuncin da ke jiran sojojin, ya yi albishir ga iyalansu

Source: Twitter
Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar Turkiyya, TRT World.
Gwamnati za ta kula da iyalan sojoji 16
Janar Musa ya bayyana cewa yayin da jami’an da ake zargin za su fuskanci shari’a a gaban kotun soja, gwamnati tana sane da bukatar kula da jin dadin wadanda suke karkashinsu.
Ministan ya ce:
"Kowa ya san irin sakamakon da ke biyo baya idan mutum ya aikata irin wadannan laififfuka (na juyin mulki) don haka na tabbata sun riga sun yanke shawara a ransu.
“Ya kamata a ce sun tuna iyalansu kafin su yi haka, amma gaskiyar ita ce, har a manyan dakarun sojoji, gwamnati tana tabbatar da cewa ana kyautata wa iyalansu.”
Za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu
Ya bayyana cewa jami’an da ake zargi da hannu a makarkashiyar za su fuskanci shari’ar kotun soja kamar yadda doka ta tanada, kuma za a ba su damar kare kansu.
“Don haka za su fuskanci kotun soja kamar yadda aka saba. Shari’ar za ta kasance cikin gaskiya da adalci; za a ba su damar daukar nasu lauyoyin don kare su,” in ji Musa.
Ministan tsaro ya kara da cewa jin dadin iyalan jami’an sojoji na cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta sa a gaba.
“Ba za mu bar ’yan uwansu su kadai ba. Gwamnati tana kokarin ganin akalla an kula da su. Ya kamata a kula da mata da yara,” in ji shi.

Source: Facebook
Wadannan kalamai nasa sun biyo bayan tabbatarwar da Hedikwatar Tsaro ta yi kwanan nan cewa an kama jami’an soja 16 da wasu fararen hula dangane da yunkurin juyin mulki ga Tinubu.

Kara karanta wannan
Kanal Ma'aji: Abin da muka sani kan sojan da ya jagoranci yunkurin kifar da Tinubu
Wannan ya faru ne bayan da sojoji suka musanta hakan a watan Oktoban 2025 lokacin da rahotanni suka fara fitowa kan kama jami'an, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Yadda aka sayo motoci da nufin juyin mulki
A wani rahoton, kun ji cewa bincike ya bankado yadda wadanda suka shirya kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka sayo sababbin motoci samfurin SUV.
Majiyoyin tsaro da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa masu bincike sun gano hujjojin sayen motocin da abubuwan da aka yi da su.
Ana zargin an yi amfani da motocin wajen jigilar jami’an da ke cikin shirin ba tare da janyo hankalin jama’a ba, da kuma gudanar da sintiri na leken asiri.
Asali: Legit.ng
