Gwamna Ya Tube Rawanin Sarki, Ya Kori Wasu Jami'an Gwamnati daga Aiki

Gwamna Ya Tube Rawanin Sarki, Ya Kori Wasu Jami'an Gwamnati daga Aiki

  • Gwamna Francis Nwifuru ya fusata matuka kan mummunan farmakin da aka kai kauyen Okporojo, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane hudu
  • Rahotanni sun nuna cewa mutanen garin Amasiri ne suka kai harin, saboda rikicin da ke tsakaninsu da kauyen Okporojo
  • Gwamna Nwifuru ya tsige sarkin yankin tare da korar duk wani dan garin Amasiri da ke rike da mukami a gwamnatinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi, Nigeria - Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya soke daukacin tsarin shugabancin siyasa da na gargajiya na al’ummar Amasiri da ke karamar hukumar Afikpo.

Wannan mataki ya biyo bayan wani mummunan rikici da ya afku a kauyen Okporojo, yankin Oso Edda da ke karamar hukumar Edda a ranar Alhamis, inda rahotanni suka ce an guntule kan mutane hudu.

Gwamna Nwifuru.
Gwamna Francis Nwifuru yayin zaman Majalisar zartarwa ta jihar Ebonyi Hoto: Rt. Hon. Francis Nwifuru
Source: Facebook

Abin da ya fusata gwamnan Ebonyi

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ana zargin mutanen garin Amasiri da kai farmaki kauyen sakamakon rikicin iyaka da ya dade yaa ci tsakaninsu da mutanen Okporojo.

Harin da aka kai ya yi sanadiyyar lalata gidaje da kaddarori na miliyoyin Nairori a yankin, lamarin da ya fusata mai girma gwamna.

Gwamna Nwifuru ya sanar da wadannan tsauraran matakai ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyarar gani da ido kauyen Okporojo, inda ya tattauna da mazauna yankin, shugabannin al’umma, jami’an tsaro, da ma’aikatan gwamnati.

Gwamna Nwifuru ya nuna bacin ransa

Nwifuru, wanda aka ga alamun bacin rai a tare da shi, ya bayyana harin a matsayin "abin takaici kwarai" kuma ya ce bai taba tsammanin ganin irin wannan zalunci a jiharsa ba.

Ya tabbatar wa al’ummar da abin ya shafa cewa gwamnati za ta dauki mataki mai tsauri kan wadanda ke da hannu.

"Wannan lamari ya kona mini rai kwarai. A matsayina na jagora mai taka-tsantsan, idan ina cikin fushi, ba na yawan magana.
"Amma ina so in tabbatar muku cewa gwamnatin jihar Ebonyi za ta nuna wa wadanda suka aikata wannan danyen aiki ainihin ma'anar gwamnati," in ji Gwamnan.

Kara karanta wannan

Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito

Gwamnan ya bayyana cewa rikicin ya kwashe shekaru yana ci duk da kokarin sasanci da aka yi, ciki har da yarjejeniyar iyaka, amma abin takaici ba a mutunta yarjejeniyoyin ba.

Gwamna ya tsige sarki da hadimansa

Domin nuna bacin ransa da kuma tabbatar da doka, Gwamna Nwifuru ya ba da umarnin rushe kungiyar cigaban garin Amasiri da daukacin shugabanninta, cewar rahoton Vanguard.

Gwamnan ya kuma soke takardar shaidar zama sarki ta sarkin gargajiya na yankin tare da tsige dukkan masu rike da sarauta a karkashin masarautar Amasiri.

Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francia Nwifuru a fadar gwamnatinsa Hoto: Rt. Hon. Francia Nwifuru
Source: Facebook

Ya kuma kori daukacin masu rike da mukaman siyasa da suka fito daga Amasiri, tun daga mambobin kwamitocin gudanarwa har zuwa matakin Kwamishinonin da ke aiki a gwamnatinsa.

Gwamnan Ebonyi ya dawo da jami'an gwamnatinsa

A wani rahiton, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sassauta kan matakin da ya dauka na ladabtar da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa.

Francis Nwifuru ya dage dakatarwar da ya yi wa kwamishinoni 25 da wasu jami'an gwamnati kan kin halartar wani muhimmin taro na gwamnatin Ebonyi.

Gwamna Francis Nwifuru dai ya hukunta jami'an gwamnatin ne saboda gazawa wajen halartar taro, lamarin da ya ce ba zai lamurta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262