'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, an Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, an Kashe Bayin Allah

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun sake farmakar mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Zamfara
  • Mugayen 'yan bindiga sun hallaka mutane tare da jikkata wasu yayin wani farmaki da suka kai a kauyen karamar hukumar Tsafe
  • Hakazalika, 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da wani adadi na mutanen da ba a sani ba zuwa cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun hallaka akalla mutane shida yayin da wasu da dama suka jikkata, yayin wani hari a Zamfara.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Kanbiri ta hanyar Kwaren Ganuwa a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, a yammacin ranar Alhamis, 29 ha watan Janairun 2026.

'Yan bindiga sun kashe mutane a jihar Zamfara
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kai hari kasuwa a Yobe bayan samun bayanai kan Boko Haram

'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara

Mazauna yankin sun ce maharan sun mamaye kauyen da misalin karfe 2:50 na rana, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.

Wani mazaunin yankin ya ce:

"Sun harbi mutane da yawa. An tabbatar da mutuwar mutane shida nan take, yayin da wasu suka samu raunukan harbin bindiga.”

An kuma ruwaito cewa maharan sun yi awon gaba da adadin mutanen da ba a tantance ba, inda suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Sojoji sun kai dauki

Tun bayan faruwar lamarin, sojoji da sauran jami’an tsaro sun isa yankin domin kwashe gawarwaki don yi musu jana’iza, tare da fara kokarin bincike da ceto wadanda aka sace.

Kauyen Kanbiri da makwabtansa a karamar hukumar Tsafe sun sha fama da hare-hare a watannin baya-bayan nan, yayin da kungiyoyin ’yan bindiga ke ci gaba da kai hari kan kauyuka a fadin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Masu safarar makamai ga tantirin jagoran 'yan bindiga sun shiga hannun jami'an tsaro

'Yan bindiga sun sake kai hari

A wani lamari makamancin haka, mutane hudu sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan ’yan bindiga sun kai hari kauyen Karakkai a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga kauyen da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Alhamis, inda suka rika harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya haddasa firgici a tsakanin al’umma.

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kona mutane a harin 'yan bindiga

An ce mazauna kauyen sun yi turjiya ga maharan, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigan janyewa daga Karakkai.

Sai dai daga bisani maharan sun wuce kauyen Gwargwabe da ke gundumar Nahuche a wannan karamar hukuma, inda suka kone gidaje da dama.

Sakamakon wannan kone-kone, mutane hudu sun kone kurmus, yayin da dabbobi kimanin 10 da kuma rumbunan hatsi akalla 50 suka lalace gaba daya.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun farmaki jami'an 'yan sanda da suka fito bakin aiki a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Harin da 'yan bindigan suka kai a kan hanyar Guga-Bakori ya jawo 'yan sandan Najeriya huɗu sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata.

Majiyoyi sun bayyana cewa direban motar sintirin ya rasa ikon sarrafa ta ne bayan da aka soma harbe-harbe, lamarin da ya sa motar ta kife a gefen hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng