Tsohon Minista Ya Yi Bayanai, Ya Fadi Abin da Ya Hana Buhari Magance Rashin Tsaro da Cin Hanci

Tsohon Minista Ya Yi Bayanai, Ya Fadi Abin da Ya Hana Buhari Magance Rashin Tsaro da Cin Hanci

  • Tsohon Ministan sadarwa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya yi magana kan matsalar rashin tsaro
  • Adebayo Shittu ya bayyana talauci da albarkatun da ke cikin daji watau ma'adanai na taka rawa wajen karuwar matsalar rashin tsaro
  • Ya kuma yi tsokaci kan abubuwan da suka hana Muhammadu Buhari magance matsalolin rashin tsaro da cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya yi tsokaci kan matsalolin rashin tsaro.

Adebayo Shittu ya kuma yi magana kan dalilin da ya sanya marigayi Muhammadu Buhari ya kasa magance matsalar rashin tsaro da cin hanci.

Adebayo Shittu ya ce Buhari ya gaza magance rashin tsaro
Marigayi Muhammadu Buhari da tsohon Ministan sadarwa, Adebayo Shittu Hoto: Muhammadu Buhari, Adebayo Shittu
Source: Facebook

Adebayo Shittu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Leadership wadda aka wallafa a ranar Asabar, 31 ga watan Janairun 2026.

Ministan Buhari ya yi tsokaci kan rashin tsaro

Kara karanta wannan

'Na hango shi a karagar mulki': An 'fadi' gwamnan da zai gaji kujerar Tinubu

Tsohon Ministan ya bayyana cewa matsalolin rashin tsaro suna da alaka da tsabagen talauci da ya yi wa mutane katutu.

“Dalilan ayyukan 'yan bindiga da rashin tsaro a Najeriya suna da bangarori biyu. Na farko shi ne gargadin da marigayi Cif Obafemi Awolowo ya taba yi, cewa idan ba a kula da ’ya’yan talakawa ba, idan suka girma ba za su bari ’ya’yan masu hali su yi barci cikin kwanciyar hankali ba."
"Idan aka bar yara ba tare da ilimi ba, su girma su gano babu abin da rayuwa ta tanadar musu; ba su da aiki, ba su da rayuwar iyali, ba su da komai, kuma ba su iya dacewa cikin al’umma ba."
"A cikin irin wannan hali na yanke kauna, abin da ya rage musu shi ne su shiga yaƙi da al’umma, wato tawaye ga al’umma.”
“Wannan ne dai abin da ke faruwa a yau, musamman a Arewa. Don haka, da wuri-wuri a samar da ilimi kyauta kuma dole a dukkan matakai a fadin kasar nan, shi ne mafi alheri gare mu. Idan muka ki yin hakan, to al'umma da za ta zo a nan gaba ma za su fada harkar fashi da makamantansu.”

Kara karanta wannan

Hadimin Shugaban kasa: Abin da ya kai Bola Tinubu Turkiyya daga dawo wa Najeriya

“Dalili na biyu kuwa shi ne bayan talauci, akwai tarin albarkatun ma’adanai da ke boye a dazuzzuka, inda da dan kokari kadan mutum zai iya zama mai kudi."
"Saboda haka, wasu masu wayo kan hada kai su dauki marasa aikin yi domin su yi musu dabaru. Wadannan su ne manyan matsaloli biyu da Najeriya ke bukatar ta warware.”

- Adebayo Shittu

Me Adebayo Shittu ya ce kan Buhari?

Da aka yi tambaye shi ko gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari wadda ya yi aiki a cikinta ko ta magance rashin tsaro da cin hanci, sai ya ka da baki ya ce:

“To, bisa gaskiya da mutuntawa bai cika sharuddan da ake bukata domin cimma wadannan manufofi ba, kuma ina fadar haka ne cikin girmamawa gare shi.”
“Na farko, mutum ne mai shiru sosai. Na biyu, ba mutum ba mai cudanya da jama’a ba. Na uku, yana da yawan yarda da mutanensa ba tare da isasshen sa ido ba."
"Na hudu kuma, yana barin abubuwa ga kaddara, irin salon da ake cewa komai sai Allah Ya yi. Saboda haka, a bangaren yaki da cin hanci, ina ganin bai yi nasara ba.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya zagi tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadi Buhari? An samu bayanai

“Mutanen da ke kewaye da shi sun yi amfani da wannan halin na sa na yin shiru da rashin magana suka yi ta tatsar albarkatun kasa ta hanyar cin hanci da rashawa."
"Hatta a bangaren tsaro, akwai bayanai kan biliyoyin daloli da aka ware domin sayen kayan aiki da biyan sojoji da ke fagen daga.”
“Amma sai aka rika jin koke-koken sojoji a fagen daga cewa ba a biyansu hakkokinsu yadda ya kamata ba. Ban ga wani mataki mai tsauri da ya dauka ba. Don haka, abin takaici ne."
"Amma yanzu ya rasu, ya dace mu bar maganarsa mu mayar da hankali kan gwamnatin da ke kan mulki. Duk abin da bai kammala ba, yanzu akwai sabuwar gwamnati da ke da nauyin kammala wadannan manufofi yadda ya dace.”

- Adebayo Shittu

Adebayo Shittu ya yi maganganu kan matsalar rashin tsaro
Tsohon Ministan sadarwa, Adebayo Shittu Hoto: @onejoblessboy
Source: Twitter

Dalilin da ya sa Buhari ya kori Hadiza Bala

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai magana yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya tuna baya kan korar da Muhammadu Buhari ya yi wa Hadiza Bala Usman daga shugabancin hukumar NPA.

Garba Shehu ya ce Buhari ya karɓi wasiƙa daga Rotimi Amaechi inda ya nemi a dakatar da Hadiza Bala Usman daga aiki.

Ya ce a cewar Amaechi, an bayar da shawarar dakatar da Hadiza Bala Usman ne sakamakon zargin cewa hukumar NPA ta kasa mayar da N165bn na ribar aiki cikin asusun gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng