Barawon Motar Naira Miliyan 75 Ya Yi wa 'Yan Sanda Barkwanci a Kano

Barawon Motar Naira Miliyan 75 Ya Yi wa 'Yan Sanda Barkwanci a Kano

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke mutum uku bisa zargin sayen wata mota kirar Mercedes Benz GLE da alat na bogi a FCT, Abuja
  • Binciken farko ya nuna barayin sun saye motar ne a yankin Gwarinpa, Abuja, kan kudi Naira miliyan 75 ta hanyar tura sakon kudi na bogi
  • Daya daga cikin wadanda aka kama, Jamilu Auwal ya yi wa 'yan sanda shakiyanci yayin da ake masa tambayoyi kan shaye shaye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutum uku da ake zargi da hannu wajen sayen mota ta hanyar amfani da alat na bogi, a wani samame da aka kai a unguwar Kabuga cikin birnin Kano.

Rahoton rundunar ya bayyana cewa an kama su ne a ranar 28, Janairu, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka shafi wata mu’amala ta kudi da ake zargin taudiyya ce.

Kara karanta wannan

An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki

Kakakin 'yan sandan jihar Kano
Kakakin 'yan sanda da motar da aka kwato a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa hirar da suka yi da barawon a wani sako da ya wallafa a Facebook.

An kama barayin mota a Kano

A cewar sanarwar rundunar, sashen SIS ne ya gudanar da aikin, karkashin jagorancin kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori.

Jami’an sun yi aiki ne bisa bayanan sirri da aka samu kafin su cafke Ibrahim Tijjani, Jamilu Auwal da Mohammed Nura Dauda a birnin Kano.

Ana zargin mutanen uku da sayen wata mota kirar Mercedes Benz GLE, mai launin fari, ta hanyar amfani da alat na bogi ga dan kasuwa a Abuja.

Daya daga cikin barayin ya ce ya tura sakon alat din ne domin yaudaran mai motar, lamarin da ya kai ga mika motar ba tare da karbar kudi na gaskiya ba.

Bayan kama su, jami’an tsaro sun kwato motar tare da mika ta ga rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Barawo ya yi wa 'yan sanda shakiyanci

A yayin tambayoyi da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi wa daya daga cikin wadanda ake zargi, Jamilu Auwal, an samu wani yanayi na shakiyanci.

Da aka tambaye shi ko yana shaye-shaye, ya bayyana cewa yana shan abubuwa da yawa:

"Shekarana 32, gaskiya ina ashan abubuwa da yawa, ina shan madara, bornvita, wallahi yallaboi wani lokacin har fura da nono ina sha."
Kakin 'yan sandan jihar Kano
Abdullahi Kiyawa da ke magana da yawun 'yan sandan Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Yadda aka gudu da motar a Abuja

Binciken farko da 'yan sanda suka yi ya nuna cewa an sayi motar ne a yankin Gwarinpa, Abuja, kan kudi Naira miliyan 75.

Ana zargin wani mutum mai suna Ibrahim Yahaya, wanda har yanzu ya tsere, da tura alat na bogi da aka yi amfani da shi wajen sayen motar.

Kwamishinan ’yan sandan ya yaba da jajircewa da kwarewar jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da zama masu sa ido.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bankado masana'antar kera bindigogi, an cafke makeri

An kama matashi da bindiga a Kano

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da ya mallaki bindiga da harsashi ba bisa ka'ida ba.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa matashin ya dawo gida da bindigar ne bayan ya tafi hutun karshen shekara wani gari.

Ya yi wa mahaifiyarsa dukan tsiya a dalilin kwace bindigar da ta yi a jakarsa, wanda ya gudu kafin daga bisani hukuma ta kama shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng