Mutum 2 Sun Mutu a Hanyar zuwa Jana'izar Mataimakin Gwamnan da Ya Rasu a Najeriya

Mutum 2 Sun Mutu a Hanyar zuwa Jana'izar Mataimakin Gwamnan da Ya Rasu a Najeriya

  • A yau Juma'a, 30 ga Janairu, 2026 aka yi jana'izar mataimakin gwamnan Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya rasu a watan Disamba, 2025
  • Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu sun mutu a hanyarsu ta zuwa wannan jana'iza a garin garin Ofoni da ke Karamar Hukumar Sagbama, a jihar Bayelsa
  • Hukumar 'yan sanda da gwamnatin jihar Bayelsa sun tabbatar da aukuwar hatsarin, sun ce ana ci gaba da tantance wadanda mummunan lamarin ya shafa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa, Nigeria - An shiga jimami a jihar Bayelsa yayin da ake shirye-shirye da bukukuwan bankwana ga marigayi tsohon mataimakin gwamna, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum 2 ne aka tabbatar da sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar zuwa wurin jana'izar mataimakin gwamnan.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Yan sanda sun kutsa cikin masallacin Juma'a, sun kama malamin Musulunci

Sanata Ewhrudjakpo.
Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Marihayi Sanata Ewhrudjakpo Hoto: Senator Lawrence Ewhrudjakpo
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa hatsarin ya auku ne a ranar Juma’a, 30 ga watan Janairu, 2026 a kan hanyar Toru-Orua da ke tsakanin Sagbama da Ekeremor a jihar Bayelsa.

Hatsari ya lakume rayuka a Bayelsa

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, wata motar bas mai cin mutum 18 wadda ke dauke da fasinjoji zuwa wurin jana’izar ta gamu da hatsari.

An shirya gudanar da jana'izar marigayin ne a garin Ofoni da ke Karamar Hukumar Sagbama, a jihar Bayelsa

Sai dai mutanen da ke hanyar zuwa wurin domin yi wa Sanata Ewhrudjakpo bankawana na karshe sun gamu da hatsari, inda motarsu ta yi taho mu gama da wata motar haya.

Mazauna yankin sun bayyana cewa taho mu gamar motocin biyu ne ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da kuma jikkata wasu da dama.

Gwamnati da 'yan sanda sun yi magana

Kwamishinan Lafiya na Jihar Bayelsa, Farfesa Seiyefa Brisibe, ya tabbatar da rasuwar mutanen, sannan ya bayyana cewa wadanda suka ji rauni suna karbar kulawar a wani asibiti da ke kusa.

Kara karanta wannan

Jarumin Nollywood ya shiga hannu a kan zargin shirin juyin mulki

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Musa Muhammad, shi ma ya tabbatar da faruwar hatsarin, sai dai ya ce har yanzu ana kan aikin tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu.

Gwamna Douye Diri.
Gwamna Douye Diri yana ganawa da mambobin majalisar zartarwa ta jihar Bayelsa Hoto: Douye Diri
Source: Twitter

Ya kara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar Baylesa ya tura jami’ai zuwa wurin da abin ya faru domin gudanar da aikin ceto da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

An birne Sanata Ewhrudjakpo ne a ranar Juma’a, bayan da ya yanke ya fadi sannan ya rasu a ranar 11 ga Disamba, 2025.

Tsohon sanatan Bayelsa ya rasu a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da rasuwar tsohon sanatan da ya wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, John Kojo-Brambaifa a wani asibiti a Abuja.

Gwamna Douye Diri, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon sanatan, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa wanda ya nuna kwarewa da nagarta a hidimar jama’a.

Gwamnan na Bayelsa ya bukaci iyalan marigayin da al’ummarsa da su samu nutsuwa da kwarin gwiwa bisa la’akari da kyakkyawan aiki da ya yi a rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262