Bayanai Sun kara Fitowa, An Gano Wani Shiri da Masu Yunkurin Kifar da Tinubu Suka Yi

Bayanai Sun kara Fitowa, An Gano Wani Shiri da Masu Yunkurin Kifar da Tinubu Suka Yi

  • Bincike ya bankado yadda wadanda suka shirya kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka sayo sababbin motoci SUV
  • Bayanai sun nuna cewa sun sayo motocin ne domin zirga-zirga cikin sirri da leken asiri ta yadda ba za a gane abin da suke shiryawa ba
  • Bayan haka an gano wani tsohon soja da ke da hannu a makarkashiyar kifar da gwamnatin Bola Tinubu, amma ya gudu daga kasar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bayanai na ci gaba da kara fitowa kan jami'an sojoji da sauran mutanen da suka kitsa yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki amma ba su samu nasara ba.

Bincike ya gano cewa wadanda ake zargin sun kulla makarkashiyar kifar da gwamnatin Bola Tinubu sun sayi motoci guda 32 kirar SUV, domin taimaka musu wajen aiwatar da shirinsu.

Kara karanta wannan

Burgediya janar Sadiq: Bayanai da muka sani kan zargin sojan a yunkurin a 'juyin mulki'

Motocin SUV.
Motocin SUV da wani gwamna ya rabawa sarakuna a Najeriya Hoto: Yunusa Abdullahi Kaita
Source: Facebook

Yadda aka sayo motoci a shirin juyin mulki

Majiyoyin tsaro da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa masu bincike sun gano hujjojin sayen motocin.

Masu binciken sun gano cewa an sayi motocin ne domin boye zirga-zirga, tattara bayanan sirri, da kuma ba su damar shiga wurare masu muhimmanci, ciki har da filayen jiragen sama da sauran gine-ginen gwamnati.

Ana zargin an yi amfani da motocin wajen jigilar jami’an da ke cikin shirin ba tare da janyo hankalin jama’a ba, da kuma gudanar da sintiri na leken asiri.

Daya daga cikin majiyoyi ta bayyana cewa an gano takardun shaidar sayayya, gami da rasidi da bayanan hada-hadar kudi a lokacin gudanar da bincike.

Duk wadannan suna cikin hujjojin da ake tattarawa don gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun sojoji.

Wadannan takardu da Premium Times ta samu sun nuna dalla-dalla yadda aka biya kudin motocin da sauran kayan aiki, da kuma yadda aka rarraba su ga jami’an da ke cikin shirin juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Kanal Ma'aji: Abin da muka sani kan sojan da ya jagoranci yunkurin kifar da Tinubu

An gano wani tsohon soja, Adamu

Binciken ya kuma gano wani babban janar mai ritaya, mai suna Adamu, a matsayin daya daga cikin jiga-jigan da ke da alaka da wannan shiri na kifar da gwamnatin Tinubu.

Majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa mutumin ya gudu tare da wasu mutum uku da ake zargi, amma daga bisani an gano daya daga cikin wadanda suka gudu a wata kasa a Kudancin Amurka.

Sojojin Najeriya.
Babban hafsan tsaro, Janar Oluyede tare da dakarun sojojin Najeriya Hoto: DHQNigeria
Source: Facebook

A halin yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da kokarin cafke duka wadanda ke da alaka da makarkashiyar, yayin da ake ci gaba da sanya ido da hadin gwiwar jami’an tsaro na kasashen ketare.

Wadanda aka shirya kashewa a juyin mulki

A baya, kun ji cewa bincike ya nuna cewa an shirya yadda za a kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da hallaka shugaban kasa da wasu manyan jami’an siyasar Najeriya.

Rahotanni aun nuna cewa wannan yunkuri na juyin mulki, wanda ya girgiza fadar shugaban ƙasa, ya fara fitowa fili ne a ƙarshen watan Satumban 2025.

Asirin wannan shiri ya fara tonuwa ne lokacin da wani jami'in soja dake da masaniya kan shirin ya tuntuɓi tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Janar Olufemi Oluyede .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262