'Yan Ta'addan ISWAP Sun Farmaki Sansanin Sojoji da Jirage Marasa Matuka, an Yi Barna

'Yan Ta'addan ISWAP Sun Farmaki Sansanin Sojoji da Jirage Marasa Matuka, an Yi Barna

  • 'Yan ta'addan ISWAP sun sake kai harin ta'addanci kan dakarun sojojin Najeriya da ke jihar Borno a yankin Arewa maso Gabas
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun yi amfani da jirage marasa matuka a harin da suka kai kan wani sansanin sojoji cikin tsakar dare
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an kashe sojoji tare da lalata motocin aiki yayin harin da 'yan ta'addan na ISWAP suka kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - ‘Yan ta'addan ISWAP sun kai wani harin ta'addanci kan sansanin sojonin Najeriya a jihar Borno.

'Yan ta'addan masu dauke da jiragen yaki marasa matuka sun kai hari ne man wani sansanin sojoji a jihar Borno inda suka kashe sojoji da dama.

'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki sojojin Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya a cikin daji Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Reuters ta kawo rahoton cewa 'yan ta'addan sun kai harin ne da daddare kafin asubahin ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An fara fargabar matakin da Gwamna Abba zai dauka a shari'ar Ganduje bayan komawa APC

Wannan shi ne hari na biyu da aka ruwaito 'yan ta'adda sun kai kan dakarun sojoji a jihar cikin mako guda.

'Yan ISWAP sun farmaki sansanin sojoji

Kakakin rundunar soji, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce amfani da jiragen yaki marasa matuka da mayakan ISWAP ke yi a hare-haren baya-bayan nan na nuni da karuwar tsananin rikici a yankin.

A cewarsa, ‘yan ta'addan sun kai hari sansanin Sabon Gari ne kafin wayewar gari, inda suka balle katangar tsaro tare da kutsawa cikin wani bangare na sansanin na dan lokaci, tashar TRT Africa ta kawo labarin.

Yayin artabun, harin jiragen marasa matuki ya lalata motocin sojoji da dama, ciki har da wata motar tona kasa da kuma motar daukar kaya.

Ya ce sojoji sun sake kwato iko da sansanin bayan isowar karin dakarun taimako, inda suka dakile harin tare da bin sahun ‘yan ta'addan.

An rasa rayukan jami'an tsaro

Laftanar Kanal Sani Uba ya ce wasu sojoji da mambobin CJTF) sun rasa rayukansu, ba tare da bayyana adadin wadanda suka mutu ba.

Kara karanta wannan

'Sun san da zuwan mu,' Yadda aka kashe babban sojan Najeriya da jami'ai 9 a Borno

Sai dai wasu majiyoyi biyu na tsaro sun bayyana cewa akalla sojoji tara da mambobin CJTF biyu ne suka mutu, yayin da kusan mutane 16 suka jikkata.

Sojoji na kai hare-hare kan 'yan ta'adda

A wannan shekara, rundunar sojojin Najeriya ta kara zafafa hare-hare zuwa sansanonin ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas, a wani sabon farmaki da ake yi domin murkushe kungiyoyin ‘yan ta'adda.

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari a Borno
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Duk da haka, duk da yawan atisayen soja, Boko Haram da reshen ta na ISWAP na ci gaba da kai manyan hare-hare.

Jihar Borno, inda mayakan Boko Haram da ISWAP suka kara kaimi wajen kai hari kan ayarin sojoji da fararen hula, na ci gaba da kasancewa cibiyar rikicin ‘yan tada kayar baya na tsawon shekaru 17 a Najeriya.

Sojoji sin kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda bayan kai wani hari a Yobe.

Dakarun sojojin sun yi nasarar kawar da wasu ’yan ta’adda bayan wani harin da aka kai kasuwar Baimari da ke karamar hukumar Bursari a jihar Yobe.

An kai harin ne ta sama kan 'yan ta'addan bayan da aka samu sahihan bayanan sirri kan ayyukansu a cikin wata kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng