Kanal Ma'aji: Abin da Muka Sani kan Sojan da Ya Jagoranci Yunkurin Kifar da Tinubu

Kanal Ma'aji: Abin da Muka Sani kan Sojan da Ya Jagoranci Yunkurin Kifar da Tinubu

  • Bayanai na ci gaba da fitowa kan yunkurin da wasu sojoji suka yi na kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Masu bincine sun gano babban jagoran da ya jagorancin yunkurin kifar da gwamnatin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike
  • An samu bayanai kan Kanal Mohammed Ma'aji wanda aka gano a matsayin jagoran shirya yunkurin juyin mulkin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jami’an binciken soja sun gano Kanal Mohammed Ma'aji a matsayin babban jagora a yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Baya ga kasancewarsa wanda ake zargi ya tsara yunkurin juyin mulkin, jami’an bincike sun kuma yi amanna cewa shi ne ya dauki nauyin samar da kudade wajen aiwatar da shirin.

An samu bayanai kan sojan da ya so kifar da Tinubu
Kanal Mohammed Ma'aji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @emmaikumeh/Kola Sulaiman
Source: Twitter

Majiyoyin soja da suka yi magana da jaridar Premium Times sun ce masu bincike sun yi amanna cewa Ma’aji ya taka muhimmiyar rawa a matsayin mai tsara dabaru kan yunkurin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Jarumin Nollywood ya shiga hannu a kan zargin shirin juyin mulki

Kanal Ma'aji ya jagoranci shirin kifar da Tinubu

Wata majiyar ta ce Ma’aji ya nuna kwarewa wajen tsarawa, inda ta ambato yunkurinsa na a baya-bayan nan na neman a tura shi aiki zuwa ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).

“Akwai lokacin da yake neman samun hanya domin a tura shi ONSA."

- Wata majiya

A cewar wata majiyar binciken hanyoyin kudi ya kuma sanya shi a tsakiyar zargi kan yunkurin juyin mulkin.

“Shi ne ke da alhakin tura kudade zuwa ga sauran wadanda ake zargi da shirin."

- Wata majiya

Tsohon gwamna ya shiga cikin zargi

An ce daya daga cikin mu’amalar kudin da ake bincike a kai na da alaka da Timipre Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, wanda ake zargin Ma’aji na da tsohuwar alaka da shi tun daga lokacin da yake aiki a yankin Niger Delta.

Jaridar The Cable ta ce bayan cafke Ma’aji da sauran wadanda ake zargi, masu bincike sun binciki gidan Timi Sylva da ke Abuja, lamarin da ya kara janyo shakku kan yiwuwar hannunsa a matsayin abokin hadin gwiwa na farar hula a yunkurin juyin mulkin da aka dakile.

Kara karanta wannan

An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki

Majiyoyi sun ce wadanda suka hadu da Ma’aji tun bayan kama shi sun bayyana shi a matsayin wanda bai nuna nadama ba, ba tare da wata alamar dana-sanin abin da ya faru ba yayin da ake ci gaba da bincike.

Wata majiya ta ce bai bayar da hadin kai ga masu bincike ba.

Wanene Kanal Mohammed Ma’aji?

Ma’aji, mai lambar aiki N/10668, an haife shi ne a ranar 1 ga Maris, 1976. Dan asalin kabilar Nupe ne daga karamar hukumar Edati ta jihar Neja.

Ya fara horaswar soja a ranar 18 ga Agusta, 1995, kuma ya kammala a ranar 16 ga Satumba, 2000, a matsayin daya daga cikin rukunin koyon soja na 47 na kwalejin tsaro ta Najeriya (NDA).

Ma’aji ya samu kwarewar aiki da dama ne a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur, yankin da daga bisani ya zama tushen huldodinsa na sana’a da siyasa.

Bayanai na ta fitowa kan sojan da ya so kifar da gwamnatin Bola Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Ya shiga Operation Crocodile Smile II a shekarar 2017, wani babban atisayen rundunar sojojin Najeriya da aka tsara domin tinkarar rikicin ‘yan bindiga, satar mai da rashin tsaro a Niger Delta da wasu sassan Kudu maso Yamma.

Ya kuma yi aiki a Depot Nigerian Army, daga bisani ya zama kwamandan Operation Delta Safe, tare da rike mukamai masu matukar muhimmanci a fannoni daban-daban na aiki.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2

An kara masa girma zuwa Laftanar Kanal a shekarar 2013, sannan zuwa cikakken Kanal a 2017.

A lokacin da aka kama shi, Ma'aji mai shekaru 49, yana rike da mukamin kwamandan bataliya ta 19 ta rundunar sojojin Najeriya a Okitipupa, jihar Ondo.

Jarumin Nollywood ya shiga hannu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun cafke jarumin Nollywood, Stanley Amandi kan zargin hannu a yunkurin juyin mulki.

Waɗanda ake zargi da shirya juyin mulkin sun ɗauki Amandi aiki ne domin ya riƙa yaɗa farfaganda, da nufin tallata shirin da ya haɗa da kashe manyan jami’an gwamnati a shekarar 2025.

An bayyana cewa a matsayinsa na farar hula kuma mai bada umarni a fim, an nemi a yi amfani da shi wajen yada furofagandar da za ta taimaka a kifar da gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng