An Zo Wajen: Matsayar Majalisar Dokokin Kano kan Tsige Mataimakin Gwamna Abba
- Ana ci gaba da maganganu kan makomar mataimakin gwamnan jihar Kano bayan ya ki sauya sheka zuwa APC tare da Abba Kabir Yusuf
- Kwamishinan yada labarai na jihar Kano ya fito ya bukaci mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo da ya yi murabus daga kan mukaminsa
- Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana inda aka kwana kan batun gabatar mata da bukatar tunbuke Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, na fuskantar matsin lamba mai karfi daga manyan jami’an gwamnati domin ya ajiye mukaminsa.
Mataimakin gwamnan na fuskantar matsin lambar ne bayan ya ki bin sahun Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

Source: Twitter
Majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin ‘yan majalisar da ke goyon bayan gwamnan kan yiwuwar fara shirin tsige mataimakin gwamnan idan ya ki yin murabus da kansa.
Shin mataimakin Abba zai yi murabus?
Sai dai wani babban jami’i a ofishin mataimakin gwamnan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ubangidansa ba shi da niyyar yin murabus sai dai idan Sanata Kwankwaso ne ya umurce shi.
“A gaskiya, ba zai yi murabus ba. Yana jiran umarnin Kwankwaso, don haka shi ma yana cikin halin tsaka-mai-wuya."
“Zan iya gaya maka cewa tun da dadewa wasu makusantansa sun ba shi shawarar ya yi murabus, amma yana jiran umarni daga ubangidansa na siyasa."
- Wata majiya
Mece ce matsayar majalisar dokokin Kano?
A halin da ake ciki kuma, majalisar dokokin jihar Kano ta ce babu wani batu na hukuma da aka gabatar gabanta dangane da shirin tsige mataimakin gwamnan.
Mai magana da yawun majalisar, Kamal Shawai, ya ce majalisar na hutu ne a halin yanzu, kuma ba za ta dawo zaman majalisa ba sai a watan Fabrairun 2026.
Kamal Shawai ya bayyana cewa ko da yake ‘yan majalisa sun tattauna batutuwan da suka shafi sauya shekar gwamnan a tsakaninsu ba a hukumance ba, babu wata takarda ko kuduri da aka gabatar wa majalisar dangane da tsige mataimakin gwamnan.

Kara karanta wannan
Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito
“A Litinin da ta gabata, an tattauna abubuwa da dama, ciki har da sauya shekar gwamnan, sannan daga bisani ‘yan majalisar suka bayyana matsayarsuu a fili."
- Kamal Shawai

Source: Twitter
Ba a kawo batun tsige Kwamred gaban majalisa ba
Sai dai ya jaddada cewa batun tsige mataimakin gwamnan ba ya gaban majalisar a halin yanzu, yana mai cewa ayyukan majalisa sun tsaya cik saboda hutun da suke yi.
A cewarsa, duk wani mataki na hukuma kan wannan batu sai dai idan ‘yan majalisar sun koma zama.
“Da zarar majalisar ta dawo aiki a ranar 2 ga Fabrairun 2025, idan akwai irin wannan batu, tabbas za a gabatar da shi domin tattaunawa."
- Kamal Shawai
Kwankwasiyya ta magantu kan murabus din Aminu Gwarzo
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani kam kiraye-kirayen da ake yi na mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi murabus.
Kungiyar ta soki gwamnatin jihar Kano kan kiran Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya ajiye mukaminsa na mataimakin gwamna.
Kwankwasiyya ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta mayar da hankali kan mulki da yi wa al’umma hidima, maimakon rikice-rikicen cikin gida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
