Malaman Kiristoci Sun Yi Magana da Murya 1 kan Sauke Shugaban INEC
- Batun kiran a sauke shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan na ci gaba da jawo cece-kuce
- Wata kungiya ta malalmai Kiristoci ta yi watsi da bukatar a sauke Farfesa Amupitan daga shugabancin hukumar INEC
- Kungiyar ta jero wasu matsalolin da za su iya faruwa idan Shugaba Bola Tinubu ya sake Farfesa Amupitan daga kan mukaminsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Malamai Kiristoci da ke aiki a karkashin kungiyar National Christian Alliance for Good Governance in Nigeria sun yi martani kan kiraye-kirayen sauke shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan.
Kungiyar ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na sauke Amupitan, inda suka bayyana wannan bukata a matsayin wadda ta saba da tsarin dimokuradiyya kuma ta zo ba a kan lokaci ba, musamman gabanin zaben gama-gari na 2027.

Kara karanta wannan
Maganar cire shugaban INEC ta girma, CAN ta ƙalubalanci majalisar shari'ar Musulunci

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce wannan matsayar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Dean Rev. Ozumba Emmanuel Nicodemus, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026.
Me aka ce kan kiran a sauke shugaban INEC?
Da take mayar da martani kai tsaye ga majalisar koli ta shari’a, kungiyar ta yi gargadi amfani da addini wajen neman sauke shugaban INEC, tana mai cewa hakan na iya tayar da hankula maimakon karfafa dimokuradiyya.
“Muna kallon wannan matsaya a matsayin wadda ba ta dace da dimokuradiyya ba kuma babu hujja mai karfi da ke goyon bayanta."
- Ozumba Emmanuel Nicodemus
Fastocin sun jaddada cewa kiraye-kirayen daukar matakai masu tsauri kan shugabancin hukumar zabe na iya haifar da sabani tsakanin ‘yan Najeriya masu addinai da asali daban-daban.
“Amfani da wannan dandali mai daraja wajen kiran daukar irin wadannan tsauraran matakai na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan kasa masu son zaman lafiya."
- Ozumba Emmanuel Nicodemus
Tinubu ya samu goyon baya
Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nada Farfesa Amupitan a matsayin shugaban INEC, inda ta bayyana nadin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma zai amfanar da tsarin zaben kasar.
Ta ce gogewarsa a matsayin lauyan kundin tsarin mulki zai taimaka matuka wajen karfafa gaskiya da adalci a harkokin gudanar da zabe.
“Muna da yakinin cewa dumbin kwarewarsa a matsayin lauya a fannin kundin tsarin mulki zai taimaka sosai wajen inganta tsarin zabenmu."
- Ozumba Emmanuel Nicodemus

Source: Twitter
Da suke jaddada muhimmancin kare ‘yancin INEC daga duk wani matsin lamba na waje, kungiyar ta ce dole ne a kiyaye ‘yancin hukumar domin tabbatar da sahihin zabe a 2027 da ma bayan nan.
A karshe, kungiyar ta yi kira ga majalisar koli ta shari'a da ta sake nazarin matsayarta tare da rungumar hanyar hadin kai domin kare dimokuradiyya da karfafa dankon zumuncin kasa.
Martanin CAN kan sauke shugaban INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen Arewacin Najeriya ta yi martani ga masu neman a sauke shugaban hukumar INEC.
Kungiyar CAN ta gargadi cewa amfani da addini wajen tantance amincin jami’an gwamnati na iya tayar da rikice-rikicen addini a ƙasa.
CAN ta ce Farfesa Amupitan na da ‘yancin bin addininsa kamar kowane ɗan Najeriya, kuma hakan ba hujjar nuna son kai ba.
Asali: Legit.ng

