Amurka Ta Tsananta Barazana, Ta Tura Tankokin Yaki zuwa Iran

Amurka Ta Tsananta Barazana, Ta Tura Tankokin Yaki zuwa Iran

  • Shugaba Donald Trump ya ƙara tsananta barazana ga Iran, yana cewa Amurka na iya kai hari mai zaafi kuma a cikin gaggawa
  • Trumo ya ce jiragen ruwan yaki, jiragen sama masu jefa bama-bamai da mayakan yaki na Amurka sun matsa kusa da yankin Iran
  • Amurka da kawayenta sun gabatar da manyan sharruda uku da suke so Iran ta amince da su kafin duk wata yarjejeniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Amurka – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kara tsananta kalamansa kan Iran a ranar Laraba 28 ga watam Janairu, 2026.

Ya bayyana cewa idan Iran ba ta amince da bukatun da gwamnatinsa ta gabatar ba, to Amurka na iya kai mata hari cikin sauri da zai tayar da hankali.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yaki na shirin barkewa tsakanin Amurka da Iran, an yi musayar zafafan kalamai

Amurka ta kara jan kunnen Iran
ShugabanAmurka Donald J Trump, Ayotoullah Khameni Hoto: Donald J Trump/@khamenei
Source: Facebook

New York Times ta wallafa cewa wannan barazana ta zo ne a daidai lokacin da jirgin ruwan yakin Amurka na Abraham Lincoln suka nufi Iran.

Tankokin yakin Amurka sun tunkari Iran

BBC Hausa ta wallafa cewa Donald Trump ya kara da cewa wasu manyan jiragen ruwa, jiragen sama masu jefa bama-bamai da kuma mayakan yaki sun isa Gabas ya Tsakiya.

Ana sa ran idan har akwai bukatar hakan, za su iya kai hari kai tsaye zuwa Iran daga dukkanin wuraren da aka girke su.

Trump ya kwatanta wannan shiri da irin matakan da ya dauka a karshen shekarar da ta gabata a yankin Venezuela.

Trump ya ce an tura kayan yaki kusa da Iran
Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

A wancan lokaci, kasar Amurka ta tara manyan dakaru da kayan yaki kusa da kasar kafin wani aiki na musamman inda aka sace Shugaban Kasar, Nicholas Maduro.

A cewarsa, wannan sakon gargadi ne ga shugabannin Iran da su gaggauta yin sulhu kafin lamura su lalace.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Abin da Trump ke nema daga Iran

Sai dai Trump bai fayyace irin yarjejeniyar da yake nema ba. Abin da kawai ya bayyana shi ne cewa wata babbar rundunar jiragen ruwa na kan hanyarta zuwa yankin Iran.

Ya yi kira ga Tehran da ta zauna teburin tattaunawa. Duk da haka, jami’an Amurka da na Turai sun bayyana cewa akwai manyan bukatu guda uku da aka gabatar wa Iran.

A cewar wadannan jami’ai, Amurka na bukatar Iran ta dakatar da duk wani aikin tace sinadarin' uranium' har abada tare da kawar da dukkannin abin da ta riga ta tara.

Haka kuma, ana son a takaita yawan da nisan makaman linzami masu linzamin da Iran ke mallaka, sannan ta daina duk wani tallafi ga kungiyoyin da Amurka ke kira ‘yan ta'adda.

Sun hada da kungiyoyin da ke aiki a Gabas ta Tsakiya, daga ciki har da Hamas, Hezbollah da Houthi da ke Yemen.

Amurka ta sako Iran a gaba

Kara karanta wannan

Masu zanga zangar Amurka na fita kan titi da bindigogi, Trump ya damu

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya aika da sakon gargaɗi mai ƙarfi ga kasar Iran, yana mai nuna damuwa kan shirinta na nukiliya.

Trump ya bayyana cewa lokaci na ƙurewa ga Iran ta amince da shiga tattaunawa da Amurka domin cimma yarjejeniya, matakin da zai iya hana barkewar rikicin soji a yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya ce Iran na bukatar shiga tattaunawa domin cimma yarjejeniya kan shirinta na nukiliya, wanda ƙasashen yamma ke zargin ana amfani da shi ne domin kera babban bam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng