Matashin da Ya Mallaki Bindiga a Kano Ya Yi wa Mahaifiyarsa Dukan Tsiya
- Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wani matashi mai shekaru 25 bisa zargin dukan mahaifiyarsa tare da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba
- An gano bindigar ne bayan mahaifiyar tasa ta ƙi ba shi ita, abin da ya haifar da tashin hankali a gidan, lamarin da ya jawo neman taimakon gaggawa
- Kakakin rundunar ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sanda ya yaba wa jarumtar matar, tare da kira ga iyaye su ƙara sa ido kan halayen ’ya’yansu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da cafke wani matashi mai suna Ididiong James, mai shekaru 25, bisa zargin kai hari ga mahaifiyarsa tare da mallakar bindigar hannu da harsasai a cikin birnin Kano. Lamarin ya faru ne a unguwar Panshekara, inda ’yan sanda daga sashen caji ofis na yankin suka kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa daga mazauna unguwar.

Source: Facebook
Kakakin yan sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan mahaifiyar matashin ta gano bindiga a jakarsa tare da ƙin miƙa masa ita.
Matashi ya ya yi wa mahaifiyarsa duka
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa a ranar 25, Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, jami’anta sun amsa kiran gaggawa daga Panshekara Quarters a Kano.
Da isarsu gidan, sun tarar da cewa ana zargin matashin yana dukan mahaifiyarsa, sai dai ya tsere daga wurin kafin a kama shi.
Mahaifiyar tasa ce ta miƙa bindiga guda ɗaya da harsasai takwas ga ’yan sanda, tana mai bayyana cewa ta same su ne a cikin jakar ɗanta.
Karin bayani daga mahaifiyar matashin
A bayanin da ta bayar ga jami’an tsaro, matar ta nuna damuwa kan canjin halayen ɗanta tun bayan dawowarsa daga bikin sabuwar shekara.
Ta ce halayensa sun sauya, yana nuna alamun tashin hankali fiye da da, abin da ya sa ta yanke shawarar hana shi mallakar bindigar da ta gano.
'Yan sanda sun kamo matashin
Bayan tserewarsa daga wurin, rundunar ta ce an samu nasarar cafke Ididiong James daga bisani, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jarumtar mahaifiyar, yana mai cewa tsayuwarta tsayin daka ya taimaka wajen hana abin da ka iya jawo babbar illa.

Source: Facebook
Ya kuma yi kira ga iyaye da su kasance masu lura da halayen ’ya’yansu, tare da gaggauta sanar da hukumomi duk wani abu da suka ga yana da alamar barazana ga tsaro.
An daure Malamin Musulunci a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kotu a jihar ta tura Sheikh Ibrahim Isa Makwarari gidan gyaran hali bayan gurfanar da shi.
Rahotanni da aka fitar sun bayyana cewa an tura malamin kurkuku ne biyo bayan gaza cika sharudan beli da kotun ta gindaya masa.
Gwamnatin jihar Kano ce karkashin ma'aikatar kasa ta shigar da malamin kara bisa zargin almundahana da ya shafi filayen hukumomi da na jama'a
Asali: Legit.ng


