An Fara Fargabar Matakin da Gwamna Abba Zai Dauka a Shari'ar Ganduje bayan Komawa APC

An Fara Fargabar Matakin da Gwamna Abba Zai Dauka a Shari'ar Ganduje bayan Komawa APC

  • Lauya Abba Hikima ya ja hankalin gwannan Kano, Abba Kabir Yusuf game da shari'o'in da ake tuhumar Ganduje da sace kudin talakawa
  • Fitaccen lauyan ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar rufe shari'o'in bayan Gwamna Abba ya koma APC mai mulkin kasar nan
  • Ya ce wajibi ne Abba ya tabbatar an karisa wadannan shari'o'i domin kwato hakkokin jama'a da ake zargin an yi sama da fadi da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Fitaccen lauya mazaunin Kano, Abba Hikima, ya yi kira ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya tabbatar an ci gaba shari'o'in cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje.

Abba Hikima ya bukaci gwamnan Kano da kada komawarsa jam'iyyar APC ta sa a birne zargin wawure dukiyar Kano da ake yi wa Ganduje da wasu mutane na kusa da shi.

Kara karanta wannan

Bayan Abba ya shiga APC, an zakulo gwamnoni 7 da suka rage a jam'iyyun adawa

Gwamna Abba da Ganduje.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ana fargabar rufe shari'o'in Ganduje

Lauyan ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook yayin da ake ci gaba da bayyana ra'ayoyi kan sauya shekar Abba Gida-gida daga NNPP zuwa APC.

Abba Hikima, mai fafutukar kare hakkin dan adam, yana fargabar cewa za a iya rufe wasu shari'o'in da ke gaban kotu wadanda suka shafi zargin rashin gaskiya a harkar kudi da kuma mallakar kadarorin gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Abba ya fita daga NNPP a ranar Juma’a kuma ya koma APC a hukumance ranar Litinin, inda ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin amfanin al’ummar jihar Kano.

Abba Hikima ya ba Gwamna Abba shawara

Da yake tsokaci kan wannan batu, Abba Hikima ya ce sauye-sauyen siyasa a Kano na iya kaiwa ga binne zarge-zargen cin hanci da ake wa Ganduje.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Gwamna Abba ya shirya tsaf, ya bayyana ranar komawa jam'iyyar APC

"Kamata ya yi a ce da Ganduje ya zo jiya a kama shi a mika wa kotu saboda ya ki halartar zaman da ake yi, amma sai ga shi a gidan gwamnati da jami'an tsaro, abu kamar wasan kwaikwayo.
"Ina kira ga talakawa, ku bude idanunku ku ga abubuwan da suke faruwa a wannan kasar, yadda shugabanni suka dauke mu, mu san me ya kamata mu yi, kasar nan ba mu inda ya wuce ta.
"Sannan su kuma shugabanni musamman Abba Gida-Gida, ni har yanzu bai mini laifi ba, amma damuwata shi ne akwai wajibci har yanzu a kan zarge-zargen da ake wa mutanen da ake ganin cewa ba su kyauta ba, sun saci kudin al'umma.
"Wajibi ne har yanzu mutanen nan a bibiye su, a karbi hakkokin al'umma, an ce makiya Kano ne, ya kamata lallai a bibiye su, bai kamata a ce wannan abu ya wuce ba."

- Abba Hikima.

Abba Hikima da Gwamna Abba tare da Ganduje.
Lauya Abba Hikima da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da Ganduje Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

An kama shaida a shari'ar Ganduje

A wani labarin, kun ji cewa 'yan sanda sun cafke wanda ya amince zai ba da shaida a shari'ar tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da gwamnatin Kano.

Wanda aka kama shi ne babbar shaida a takaddamar mallakar tashar jirgin ruwa ta biliyoyin Naira da ta shafi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

A lokacin da aka kama shi, yana tare da Aminu Dabo, fitaccen dan siyasar Kano kuma tsohon shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262