Rashin Tsaro: Matakin da Gwamnatin Kebbi Ta Dauka don Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Rashin Tsaro: Matakin da Gwamnatin Kebbi Ta Dauka don Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta tashi tsaye don tunkarar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita sakamakon hare-haren 'yan bindiga
  • Gwamnan Nasir Idris ya amince da horaswa tare da tura 'yan banga a fadin jihar domin taimakawa wajen samar da tsaro
  • A shirin da gwamnan ya bullo da shi, za a horas da 'yan banga sannan a tura su domin taimakawa hukumomin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi: Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da horaswa tare da tura ‘yan banga 3,000 a fadin jihar.

Gwamna Nasir Idris ya amince da hakan ne domin karfafa tsaron al’umma da kuma tallafa wa hukumomin tsaro na gwamnati.

Gwamnatin Kebbi ta horas da 'yan banga
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Talata, 27 ga watan Janairun 2026 yayin da yake duba ‘yan banga 500 da mafarauta da ke karbar horaswar sabunta dabarun tsaro a karamar hukumar Kalgo.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da 'dan majalisa da wasu mutum 14 ya bace bayan tashinsa

Matakin da gwamnatin Kebbi ta dauka

Gwamna Nasir Idris ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon karuwar matsalolin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, ciki har da ‘yan bindiga, satar shanu da kuma garkuwa da mutane.

“Ayyuka sun yi wa hukumomin tsaro da ke Kebbi yawa sosai. Yanzu dole ne a horas da ‘yan banga su rika tallafa musu."

- Gwamna Nasir Idris

Gwamna Nasir ya bada shawara

Gwamnan ya bukaci mahalarta horaswar da su rika taimakawa ayyukan tsaro da zarar an tura su zuwa al’ummominsu.

Ya bayyana cewa za a horas da ‘yan banga 3,000 din ne a kashi-kashi na mutum 500 domin kauce wa cunkoson wuraren horaswa.

Gwamnan ya kara da cewa za a shigar da mata a rukuni na gaba, bisa la’akari da bukatun tsaro da kuma kara shigo da al’umma don magance matsalar.

Gwamnati za ta tallafa a murkushe 'yan bindiga

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirin ta hanyar biyan alawus-alawus akai-kai, samar da kayan aiki da kuma sa ido akai-akai.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya yi sababbin nade nade bayan ya koma APC

Gwamna Nasir Idris ya bayyana shirin a matsayin muhimmi domin tabbatar da cewa mazauna jihar za su rika kwana lafiya ba tare da fargaba ba, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Masu horaswar, wadanda aka zakulo su daga dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar, na karbar kwas na kwanaki 14 da ya kunshi dabarun tsaro, tattara bayanan sirri, kare hakkin dan Adam, taimakon gaggawa, sarrafa makamai da kuma tsarin sadarwa.

Gwamnatin Kebbi za ta tura 'yan bindiga don samar da tsaro
Gwamna Nasir Idris a wajen taron gwamnonin Arewa Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Ya tsarin samar da tsaron yake?

Da yake magana kan shirin, mai ba gwamna shawara kan tsaro, Kanal Danladi Ribah Zuru (mai ritaya), ya ce wannan horaswa na kara habaka wani shiri da aka taba yi a baya, amma a wannan karo an fadada darussa tare da inganta tsarin hadin kai.

Ya bayyana cewa gwamnan ya amince da samar da motoci 32, babura 511 da kuma kudin horaswa domin tallafa wa ayyukan filin aiki da jin dadin mahalarta, inda ya bayyana shirin a matsayin wani gagarumin sauyi a gyaran tsarin tsaro na jihar Kebbi.

Kanal Danladi ya kara da cewa ana sa ran rukunin yanzu zai kammala horaswa ranar Alhamis, yayin da ake shirin horas da sauran ‘yan banga 2,500 a matakai uku, inda sansanin jihar ke da karfin karbar mutum har 850 a lokaci guda.

Kara karanta wannan

Ayyukan da gwamnatin Kano za ta saka a gaba bayan Abba ya koma APC

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi wa 'yan sanda kwanton bauna a jihar Katsina.

Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki 'yan sandan ne lokacin da suke aikin sintiri a karamar hukumar Bakori ta jihar.

Mummunan lamarin ya jawo asarar rayukan 'yan sanda hudu tare da jikkata wasu bayan an yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng