Babbar Magana: Yaki Na Shirin Barkewa tsakanin Amurka da Iran, an Yi Musayar Zafafan Kalamai
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya ja kunne tare da yin barazana ga kasar Iran shirin da take yi na nukiliya
- Donald Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta kai hari ga Iran muddin ba ta hau kan teburin tattaunawa ba kan shirinta na nukiliya
- Sai dai, Iran ta mayar da martani mai zafi, inda ta bayyana abin da za ta yi da zarar aka tunzarata ta hanyar kai mata hari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya aika da sakon gargaɗi ga kasar Iran kan shirinta na nukiliya.
Donald Trump ya yi gargadin cewa lokaci na ƙurewa ga Iran ta zauna kan teburin tattaunawa domin kauce wa ɗaukar matakin soji daga Amurka.
Hakan na kunshe ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, wadda aka.sanya a Facebook a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Trump na iya kai hari Iran
Trump bai kawar da yiwuwar kai hari ba kan Iran bayan zanga-zangar da ta fara a karshen watan Disamban 2026 kuma ta kai kololuwa a ranakun 8 da 9 ga Janairun 2026.
Wata kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ce fiye da mutane 6,200 suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar.
A watan Yunin bara, Amurka ta kai hare-hare kan wuraren shirye-shiryen nukiliyar Iran a yayin yaƙin kwanaki 12 da Isra’ila ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wane gargadi Trump ya yi wa Iran?
A sakon da ya wallafa, Trump ya ce Iran na bukatar shiga tattaunawa domin cimma yarjejeniya kan shirinta na nukiliya, wanda ƙasashen yamma ke zargin ana amfani da shi ne domin kera babban bam.
“Da fatan Iran za ta gaggauta ‘zaunawa kan teburin tattaunawa’ domin yin yarjejeniyar adalci ta 'babu makaman Nukiliya' wadda za ta amfanar da kowa. Lokaci na ƙurewa, kuma lamarin na da matuƙar muhimmanci!"
“Harin da zai biyo baya zai fi muni sosai! Kada ku sake bari hakan ta faru."
- Donald Trump
A halin yanzu, wata babbar rundunar jiragen ruwan yaki ta Amurka da Trump ya bayyana a matsayin “armada”, ƙarƙashin jagorancin jirgin ruwan ɗaukar jiragen sama USS Abraham Lincoln, na shawagi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wane martani Iran ta yi?
A martaninta ga kalaman Trump, ofishin jakadancin Iran a majalisar dinkin duniya ya wallafa hoton barazanar a shafin X, tare da rubuta cewa:
“A karo na karshe da Amurka ta yi kuskuren faɗawa yake-yake a Afghanistan da Iraki, ta ɓarnatar da sama da dala tiriliyan 7 tare da rasa rayukan Amurkawa fiye da 7,000.”
“Iran a shirye take ta shiga tattaunawa bisa mutunta juna da muradu na bai ɗaya, amma idan aka tursasa, za ta kare kanta kuma ta mayar da martani ta hanyar da ba a taba gani ba!."
Gargadin da aka yi wa Trump kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jami'an Isra'ila da na kasashen Larabawa, sun ja kunnen Donald Trump kan kai hari a Iran.
Jami'an sun bayyana cewa, a fahimtarsu gwamnatin Iran na fuskantar matsin lamba amma har yanzu ba ta kai matakin rushewa ba.
Hakazalika, jami'an sun yi amanna cewa hari daga waje zai iya kasa cimma burin da ake nema na kawo sauyi cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng

