'Dan Bindiga da Ya Hana Turji, Yaransa Sakewa Ya Mutu, an Kashe Shi wurin Sulhu

'Dan Bindiga da Ya Hana Turji, Yaransa Sakewa Ya Mutu, an Kashe Shi wurin Sulhu

  • An kashe shahararren dan bindiga a wani kwanton bauna da ake alakantawa da yaran Bello Turji a cikin yankin jihar Katsina
  • Rahotanni sun ce an janyo dan ta'addan zuwa taron sulhu ne, amma aka farmake shi tare da wasu yaransa a hanyarsu zuwa zaman
  • Masana tsaro sun gargadi cewa kisan na iya jawo sabon rikici a yankin Jibia, tare da barazanar sace-sace da kuma hare-hare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jibia, Katsina - An kashe wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga kuma mai son aiwatar da da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati.

Marigayi Abdullahi Lantai, wanda aka fi sani da “Lantai Officer” na gaba-gaba wurin goyon bayan sulhu a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

An kashe dan bindiga da ke goyon bayan sulhu da gwamnati
Taswirar jihar Katsina da ake fama da yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaran Bello Turji sun hallaka 'dan bindiga

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama a yau Laraba cewa an kashe Lantai ne a ranar 27 ga Janairu da misalin karfe 1:00 na rana.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bankado masana'antar kera bindigogi, an cafke makeri

Lamarin ya faru ne a wani kwanton bauna da ake zargin ‘yan bindigar da ke biyayya ga kungiyar Bello Turji ne suka kai.

A cewar majiyoyin, an yaudari Lantai zuwa abin da aka bayyana a matsayin taron tattaunawa da sulhu, biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin kungiyarsa da ta Turji a ranar 24 ga Janairun 2026.

“Rahotanni sun nuna cewa Turji da Aliyu Aliero ne suka shirya taron domin sasanta rikicin. Sai dai Lantai da wasu daga cikin yaransa sun fada tarkon kwanton bauna, inda aka kashe su a hanyarsu ta zuwa wurin taron.”

- In ji wata majiya

Yaran Bello Turji sun hallaka wani babban dan bindiga
Marigayi Lantai da yaran Bello urji suka hallaka a Katsina. Hoto: Legit.
Source: Twitter

Kokarin neman sulhu da Lantai ya yi

Binciken farko ya nuna cewa kafin kisan nasa, Lantai ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta wucin gadi a Jibia, tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina.

Majiyar ta ce Lantai shi ne ke rike iko a yankin, inda ya hana kungiyar Turji samun ‘yancin zirga-zirga da ayyuka a cikin dazukan Jibia.

Majiyar ta ce:

“Haka kuma, ya toshe hanyoyin safarar shanun sata daga Zamfara zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya rage karfin ayyukan Turji a yankin.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

“Wannan yunkuri ne na karbe iko. Kungiyar Turji na neman kawar da wani ginshikin zaman lafiya domin fadada tasirinta, hanyoyin safara da tattalin arzikinta zuwa cikin jihar Katsina.”

Masana tsaro sun gargadi cewa kisan Lantai na iya haddasa tsanantar rikici da tashin hankali a yankin Jibia da kewaye.

A halin yanzu, an kimanta matakin barazana a yankin Jibia a matsayin mai tsanani, tare da alamun yiwuwar ramuwar gayya daga bangaren kungiyar Lantai.

Bello Turji ya kidime, ya shiga daji

Mun ba ku labarin cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dan ta'adda, Bello Turji, wanda ake nema ruwa a jallo, na fuskantar matsin lamba mai tsanani.

Babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ya ce bayanan sirri na nuna cewa Turji da mutanensa na ta kaura lokaci zuwa lokaci saboda firgita.

Sojoji sun kuma yi watsi da rade-radin cewa Turji na da iko da wasu kananan hukumomi, suna masu kiran hakan farfagandar ‘yan ta’adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.