Juyin Mulki: Yadda Kanal na Soja Ya Tsara Kifar da Gwamnatin Bola Tinubu
- Rahoton bincike ya bayyana yadda wani Kanal a rundunar sojin kasa ya tsara hanyar sadarwa tsakanin sojoji domin juyin mulki a Najeriya
- An ce yunkurin ya samo asali ne daga bakin cikin rashin samun karin matsayi, wanda daga bisani ya rikide zuwa shirin daukar matakan tsaro
- Hukumomin tsaro sun ce sun gano shirin tun kafin ranar aiwatarwa, inda aka cafke jami’ai tare da kwato muhimman takardu a wajensu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Sababbin bayanan sirri sun yi karin bayanai kan yunkurin juyin mulki da aka ce an shirya wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda hukumomin tsaro suka dakile tun kafin ya kai ga matakin aiwatarwa.
A watan Oktoba, 2025 ne jita-jitar yunkurin juyin mulki ta bazu a kafafen sada zumunta, sai dai a wancan lokaci hedikwatar tsaro ta karyata zargin.

Source: Twitter
Rahoton binciken wucin-gadi da jaridar Punch ta gani ya nuna cewa wani Kanal mai aiki a rundunar sojin kasa ne ake zargi da jagorantar yunkurin, bayan ya gaza samun karin matsayi sau da dama bayan jarrabawa.
Yadda Kanal ya tsara juyin mulki
Rahoton ya ce Kanal din ya juya damuwar da ya ke ciki zuwa wata dabara ta daukar sababbin mutane, inda ya fara tuntubar jami’ai daga rundunar sojin kasa, ruwa da ta sama domin samar da wata hanyar sadarwa.
An ce wadanda ya shigar sun fara ne da tattauna korafe-korafe kan aiki, kafin daga bisani su koma tattara bayanai kan muhimman wuraren tsaro a kasar nan, ciki har da fadar shugaban kasa da manyan sansanonin soja.
Rahoton ya bayyana cewa an raba wa mambobin aikin nazarin hanyoyin shiga, lokutan tsaro da wuraren da ake ganin suna da rauni, abin da ke nuna cewa shirin ya wuce maganar fatar-baki zuwa matakin tsari.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Abubuwan da aka gano yayin bincike
Majiyoyin tsaro sun ce yayin binciken motar Kanal din, an samu wasu kayayyakin da ke nuna adawa da gwamnati, yayin da aka samu takardu masu muhimmanci a gidansa da ke Lokogoma, Apo.
Takardun sun kunshi rabawa mutane ayyukan da za su yi da yadda za a kawar da manyan jami’an gwamnati da zarar an fara aiwatar da shirin, lamarin da hukumomi suka ce ya nuna hatsarin da shirin ke dauke da shi.
Bincike ya kuma nuna cewa an yi amfani da hanyoyin sadarwa a boye domin tsara ayyuka, daukar nauyin kudi da gyaran motoci, tare da wasu kudi da ba a saba gani ba da suka nuna an yi babban shiri.
An ba jama'a kudin juyin mulki
Rahoton ya ce wasu daga cikin manyan masu ruwa da tsaki sun karbi kudi tsakanin Naira miliyan 2 zuwa Naira miliyan 5, inda ake bibiyar hanyoyin kudin ta hannun Hukumar Leken Asirin Kudi ta Kasa.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu 'ya amince' da kirkiro sabuwar jiha 1 a Najeriya, an bayyana sunanta
Vanguard ta bayyana cewa wani jami’i, Laftanar Kanal S. Bappah, ya amince da laifinsa, inda ya bayar da bayanai kan yadda ake daukar mutane, hanyoyin kudi da tsarin sadarwa.

Source: Facebook
Hukumomin tsaro sun ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda shirin ya hada jami’ai daga rundunoni daban-daban, har zuwa matakin Birgediya Janar.
An ce an gano shirin ne kafin ranar 25, Oktoba, 2025 da aka tsara aiwatarwa, inda rahotanni suka nuna cewa shugaba, Kashim Shettima, ministoci da shugabannin tsaro na cikin jerin wadanda ake da niyyar kawarwa.
Juyin mulki: Halin da sojoji ke ciki
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kungiya a jihar Nasarwa ta yi zargin cewa sojojin da aka kama saboda yunkurin juyin mulki ba su da lafiya.
Kungiyar ta bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali kuma har yanzu ba a ba su dama sun gana da iyalai ko 'yan uwansu ba kwata-kwata.
Ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu, hukumomi da masu ruwa da tsaki a kan a sake su ko kuma a gurfanar da su idan ana tuhumarsu da wani laifi.
Asali: Legit.ng
