Tsautsayi: Mummunan Hadari Ya Rutsa da Mahaifin Kyaftin din Najeriya, Ya Rasu
- An tabbatar da mutuwar mahaifin kyaftin din tawagar Super Eangles ta Najeriya sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a Delta
- Kungiyar Besiktas da ke kasar Turkiyya ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwada ta fitar domin jajantawa dan wasanta, Nadidi
- Ndidi, wanda ke bugawa Besiktas kwallo yana yawan magana kan mahaifinsa, wanda ya ce shi ne silar nasararsa a rayuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles, Wilfred Ndidi, ya yi babban rashi biyo bayan rasuwar mahaifinsa, Sunday Ndidi.
Rahotanni sun bayyana cewa mahaifin nasa, wanda tsohon jami'in soja ne, ya rasu sakamakon hadarin mota mai muni da ya faru a ranar Talata a jihar Delta.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa hadarin ya faru ne a garin Umunede, daga bisani aka garzaya da shi asibitin Agbor, amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Ta'aziyyar kungiyarsa ta Besiktas
Kungiyar kwallon kafa ta Besiktas da ke kasar Turkiyya, wadda Ndidi ke bugawa wasa, ita ce ta sanar da wannan mummunan labari a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce:
"Muna matukar bakin cikin jin labarin rasuwar mahaifin dan wasanmu Wilfred Ndidi, Sunday Ndidi, wanda ya riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota.
"Muna rokon Allah ya jikan mamacin; muna mika ta’aziyya ga dan wasanmu Wilfred Ndidi, iyalansa, da sauran masoyansa."
Rasuwar mahaifin nasa na zuwa ne makonni bayan Ndidi ya jagoranci Najeriya wajen samun matsayi na uku (tagulla) a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025 (FACON) da aka gudanar a kasar Morocco.
Ndidi ya girmama mahaifinsa a AFCON
A gasar, Ndidi ya samu nasarar zura kwallonsa ta farko a wasannin kasashe, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.
A lokacin gasar, Ndidi ya nuna girmamawa ga mahaifinsa yayin murnar kwallon da ya zura a raga da kai a wasan da suka fafata da Tunisia.

Kara karanta wannan
Ta tabbata an yi yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki, sojojin Najeriya sun fitar da bayanai
"Na yi murnar cin kwallon da na ci saboda mahaifina, domin kullum yana yawan magana a kan Kanu Nwankwo. Sai kawai na tuna mahaifina, na ce zan yi hakan ne domin nuna girmamawa gare shi," in ji Ndidi.
Kyakkyawar alakar Ndidi da mahaifinsa
Ndidi ya sha magana kan kusancin da ke tsakaninsa da mahaifinsa, wanda ya rene shi a barikin soja.
An haifi Ndidi kuma ya girma a Legas, inda yake dora alhakin tarbiyyar da ya samu daga wurin mahaifinsa a matsayin abin da ya taimaka wajen nasarar sana’arsa ta kwallo.

Source: Twitter
Har yanzu kyaftin din na Super Eagles bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da sakonnin ta'aziyya ke ci gaba da kwarara daga wurin masoya da sauran masu ruwa da tsaki a fagen kwallon kafa.
Yadda Ndidi ya zama kyaftin a Super Eagles
A baya, kun ji cewa mahukuntan tawagar Super Eagles sun sanar da nadin dan waaan tsakiya, Ndidi a matsayin sabon kyaftin bayan ritayar Ahmed Musa.
Wilfred Ndidi mai shekara 29 ya karɓi ragamar jagoranci na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafi nasara a nahiyar Afirka.
Naɗin Ndidi ya zo ne bayan ritayar William Troost-Ekong, wanda ya kasance kyaftin din rikon ƙwarya, da kuma Ahmed Musa, wanda shi ne kyaftin na farko.
Asali: Legit.ng