APC Ta Gargadi Minista bayan Kalamanta a kan Ajiye Kashim a Zaben 2027
- APC ta gargadi ministoci da jiga-jigan jam’iyya kan tayar da jita-jita da maganganu marasa amfani, musamman game da zaben shekarar badi
- Jam’iyyar ta yi wannan jan kunne ne a lokacin da ake kara rura wutar sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin Shugaban kasa a 2027
- Gargadin ya zo jim kadan bayan Ministar al'adu da yawon bude ido, Hannatu Musawa ta ce akwai matsala idan aka ajiye Kashim Shettima a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC ta gargadi Ministar al'adu da yawon bude ido, Hannatu Musawa, da sauran manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya game da yada jita-jita.
Ta shawarci su da su daina hura wutar jita-jita marasa amfani, su maida hankali kan babban aikinsu na yi wa gwamnati da jam’iyya hidima cikin kwarewa da gaskiya.

Source: Twitter
This day ta wallafa cewa APC ta kuma yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen watsa labarai game da yiwuwar sauya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Kalaman Hannatu Musawa da suka yamutsa hazo
Jaridar Daily Post Hannatu Musawa ta yi gargadin cewa APC na iya rage karfinta matuka a zaben shugaban kasa na 2027 idan ta sauke Shettima.
Kalaman ministar sun zo ne a lokacin da ake kara rade-radin cewa jam’iyya mai mulki na iya duba yiwuwar sauya tsarin tikitin Musulmi-Musulmi da ya kai APC ga nasara a zaben 2023.
Ta yi gargadin cewa sauya Shettima ko cire Musulmi daga Arewa zai iya jawo hadari a siyasa, musamman a jihohin Arewa, inda dabi’un zabe ke da alaka da yankin da addini.
Ta ce:
“Idan babu Bahaushe, Fulani ko Kanuri Musulmi a kan wannan tikiti, hakan na haifar da cikas. Wannan shi ne yadda mutane ke tunani.”
Martanin APC ga kalaman Tinubu
Sai dai Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Felix Morka, a wata sanarwa da ya fitar, ya gargadi Ministocin gwamnatin APC a kan su mayar da hankali a kan ayyukansu.

Source: Twitter
Felix Morka ya ce:
“Muna kira ga ministocinmu, manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya da su guji tayar da jita-jita marasa amfani, su maida hankali kan babban aikinsu na yi wa gwamnati da jam’iyyarmu hidima, tare da karfafa nasarori da ayyukan Shugaba Tinubu, jagoranmu na hangen nesa.”
Jam’iyyar ta bukaci kafofin watsa labarai da su daina ba da dandalinsu ga masu yada jita-jita da majiyoyin labarai marasa tabbas.
Morka ya kara da cewa APC na ci gaba da goyon bayan Tinubu da Shettima wajen aiwatar da manufofin Bola Ahmed Tinubu don ciyar da Najeriya gaba.
APC: Hannatu ta yi magana kan takarar Kashim
A baya, mun wallafa cewa Ministar al’adu da yawon buɗe ido, Hannatu Musawa, ta shawarci jam’iyyar APC da ta yi taka-tsantsan sosai game da shirye-shiryen zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Ta bayyana cewa duk wani yunkuri na sauya tikitin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kafin babban zaɓen na iya jefa jam’iyyar cikin babbar matsala ta siyasa, musamman a yankin Arewa.
Hannatu Musawa ta kuma bayyana cewa fahimtar yanayin tunanin al’umma a Arewa abu ne mai matuƙar muhimmanci ga duk wata jam’iyya da ke son cin nasara a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

