Ganduje Ya Zagi Tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Muhammadi Buhari? An Samu Bayanai
- Kalaman da Buba Galadima ya yi cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zagi marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fara jan hankali
- Tsohon hadimin tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Oliver Okpala ya bayyana Injiniya Buba Galadima a matsayin 'dan siyasar talabijin
- Ya ce ba zai yiwu ya zuba ido yana kallo a bata sunan Ganduje, mutumin da aka san shi da tarbiyya da girmama mutane a siyasar Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Zargin da jigon NNPP, Buba Galadima ya yi cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya taba zagin marigayi Muhammadu Buhari ya fara jawo martani.
Cif Oliver Okpala, Mai taimakawa Ganduje kan wayar da kan jama'a lokacin yana shugabancin APC, ya musanta ikirarin Galadima, yana mai cewa babu inda tsohon gwamnan Kano ya taba zagi ko cin mutuncin tsohon shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Okpala ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani kan zargin da Buba Galadima ya yi wa tsohon maigidansa.
Yayin da yake siffanta Galadima a matsayin "dan siyasar talabijin" wanda ba shi da tushe a siyasance, Okpala ya bukaci Buba Galadima da ya koma jiharsa (Yobe) domin bada gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki da siyasa.
Martanin hadimin Ganduje ga Buba Galadima
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma ya raba wa manema labarai a Abuja, Okpala ya ce an san Ganduje da tarbiyya a fagen siyasa, don haka ba zai taba aibata wani kamar yadda Galadima ya yi ikirari ba.
“Na ga kalaman da aka danganta ga wani jigo a NNPP, Buba Galadima, inda ya zargi tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Ganduje, da zagin tsohon Shugaba Buhari.
“Ba zan iya yin shiru ba yayin da ake kokarin bata sunan mutum mai kishin kasa irin Ganduje duk da irin kyakkyawan suna da ya dade yana ginawa a fagen siyasar kasa da ma ta duniya."
Da gaske Ganduje ya zagi Buhari?
A rahoton jaridar The Sun, Okpala ya bayyana zargin cewa Ganduje ya taba zagin Buhari a matsayin abin dariya, yana mai cewa:
“Wannan abin dariya ne kwarai. Yana magana ne a kan mutumin da ya zama gwamnan jiha kamar Kano har sau biyu, kuma ya rike kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa.
“Damuwata ba ta siyasa ba ce, dole ne na kare mutum mai hikimar siyasa, kwarewa, da tarbiyya, musamman idan zargin ya fito ne daga bakin 'dan siyasar talabijin' wanda ba shi da mazaba, kuma bai taba tsayawa takara ko ya ci zabe ba a rayuwarsa,” in ji shi.

Source: Facebook
Yadda Buhari ya nada Lai Mohammed minista
A wani labarin, kun ji cewa Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa aminci da biyayya ne suka sanya Muhammadu Buhari ya nada shi minista har tsawon shekaru takwas.
Tsohon ministan ya bayyana haka ne a cikin littafin da ya kaddamar kan mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na tsawon shekaru takwas.
Littafin ya bankado sirrin yadda Buhari ya kira Lai Mohammed ta waya domin sanya shi a kwamitin karbar mulki daga gwamnati mai barin gado a shekarar 2015.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
