Kwanaki Kadan da Dawowa, Shugaba Tinubu Ya Sake Barin Najeriya
- Jirgin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa kasar waje 'yan kwanaki kadan bayan ya dawo gida Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya bar birnin tarayya Abuja ne a da rana a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun shekarar 2026
- Mai girma Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki ne zuwa kasar Turkiyya domin bunkasa kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin tarayya Abuja domin zuwa ziyara ta musamman a ƙasar Turkiyya.
Ziyarar Tinubu na zuwa ne yayin da Najeriya ke ƙara zurfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki da ƙasar Turkiyya.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ce jirgin shugaban kasar ya tashi daga sashen shugaban ƙasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:05 na rana a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya bar Najeriya
Tashin jirgin na nuna fara ziyarar da nufinta shi ne karfafa alakar kasashen biyu tare da faɗaɗa haɗin gwiwa a muhimman fannoni.
Daga cikin manyan jami’an da suka yi wa shugaban ƙasa rakiya zuwa filin jirgin saman akwai Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma; Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, tashar Channels tv ta kawo labarin.
Sauran su ne Ministan Abuja, Nyesom Wike; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare.
Mene ne abin da Tinubu zai yi a Turkiyya?
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a baya, ziyarar za ta mayar da hankali ne wajen ƙarfafa kyakkyawar alaƙar da ke akwai tsakanin Najeriya da Turkiyya.
Ya kuma ce ziyarar za ta binciko sababbin hanyoyin haɗin gwiwa a fannoni kamar tsaro, ilimi, ci gaban al’umma, kirkire-kirkire da harkokin sufurin jiragen sama.
A yayin ziyarar, ana sa ran Shugaba Tinubu zai yi muhimman tattaunawar siyasa da diflomasiyya da shugabannin Turkiyya, domin gina doguwar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya kawo ziyarar aiki a Najeriya a watan Oktoban shekarar 2021.

Source: Facebook
Za a gudanar da manyan tarurruka
Manufar ziyarar ta ƙunshi manyan tarurruka tsakanin jami’an kasashen biyu, tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin fahimta a fannoni kamar binciken kimiyya, makamashi, haɗin gwiwar fasaha, kafafen yaɗa labarai da sadarwa, haɗin gwiwar soji, da ka’idojin diflomasiyya.
Haka kuma za a shirya taron kasuwanci da zai haɗa masu zuba jari daga Najeriya da Turkiyya domin binciko damar zuba jari tare da karfafa alakar kasuwanci.
An ja kunnen Tinubu kan sauya Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiyar matasan APC a shiyyar Arewa maso Gabas, ta yi tsokaci kan rade-radin sauya Kashim Shettima a zaben 2027.

Kara karanta wannan
Lissafi zai iya canzawa, Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan PDP a fadar shugaban kasa
Shugaban kungiyar, Kabiru Kobi, ya bayyana cewa kokarin sauya Shettima zai iya kawo cikas ga nasarar Tinubu a yayin da zai nemi tazarce a zaben 2027.
Ya gargadi masu ruwa da tsaki da su koyi darasi daga kura-kuran baya, inda ya buga misali da yadda jam'iyyar PDP ta sha kasa a 2023, duk don saboda rikici kan takara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
