Jami'an Tsaro Sun Gwabza Fada da 'Yan Bindiga a Gombe, an Kashe 'Yan Ta'adda

Jami'an Tsaro Sun Gwabza Fada da 'Yan Bindiga a Gombe, an Kashe 'Yan Ta'adda

  • Rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar da kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, tare da kwato makamai da kuma ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace a jihar
  • Lamarin ya faru ne bayan ‘yan ta'addan sun kasa kai farmaki a wasu yankuna sakamakon tsauraran matakan tsaro, sai dai daga bisani suka kai hari a wani kauye a gefe
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce ana cigaba da bincike da farautar sauran ‘yan ta'addan da suka tsere, tare da bukatar jama’a su ci gaba da bayar da bayanai ga hukumomi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta sanar da nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen dakile ‘yan ta'adda a wasu yankunan kan iyakar jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Katsina, an kashe jami'an tsaro

Wannan na kunshe ne a cikin bayanin da kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya ce hadin gwiwar jami’an tsaro da mafarauta ya taimaka wajen dakile yunkurin ‘yan ta'addan.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A sokon da ya wallafa a Facebook, DSP Buhari ya ce lamarin ya nuna irin tsauraran matakan tsaro da rundunar ta dauka musamman a yankunan da ke kusa da iyakokin jihohi.

Yadda aka kai hari a kauyen Gombe

A cewar DSP Buhari Abdullahi, ‘yan ta'addan sun yi yunkurin kai hari a ranar Juma’a a wasu yankuna da suka hada da Pindiga, Billiri da Shongom, amma suka gaza cimma burinsu sakamakon yawaitar jami’an tsaro da aka tura yankunan.

Ya bayyana cewa:

“A ranar Juma’a sun yi kokarin kai hari, amma saboda tsauraran matakan tsaro da muka dauka a wadannan yankuna na kan iyaka, ba su samu nasara ba.”

Sai dai, a cewarsa, ‘yan ta'addan sun sake bayyana da safiyar Asabar da misalin karfe 3:00 na dare, inda suka kai hari a Garin Galadima da ke yankin Lambo, inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu biyar.

Kara karanta wannan

An wallafa bidiyon kurkukun da Boko Haram ke daure mutane a daji

An gwabza da 'yan bindiga a Gombe

DSP Abdullahi ya ce bayan samun labarin harin, jami’an ‘yan sanda, mafarauta da sauran hukumomin tsaro suka gaggauta taruwa domin bibiyar ‘yan ta'addan.

Rahotanni sun nuna cewa matakin da rundunar 'yan sanda da jami'an tsaro suka dauka ya kai ga musayar wuta mai tsanani a tsakanin bangarorin biyu.

A yayin artabun, jami’an tsaro sun samu nasarar kashe ‘yan ta'adda uku, tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, alburusai hudu, da kuma babura guda hudu da ake zargin ‘yan fashin na amfani da su wajen aikata laifuka.

An ceto wadanda aka sace a Gombe

Rundunar ta kuma tabbatar da ceto mutane uku daga cikin wadanda aka sace, sai dai daya daga cikinsu ya samu raunin harbin bindiga, wanda daga bisani ya rasu a asibiti.

DSP Abdullahi ya jaddada cewa ana ci gaba da aikin bincike domin cafke sauran ‘yan fashin da suka tsere, yana mai cewa akwai alamun da yawa daga cikinsu sun tsere da raunuka.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shiga har dajin Sambisa sun yi wa 'Yan Boko Haram jina jina

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya na bayani a jihar Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: UGC

Rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar wa da al’umma kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai da bayanai ga hukumomin tsaro.

An rusa kurkukun Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun kutsa dajin Sambisa da 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram ke fakewa.

A farmakin da sojojin Najeriya suka kai, an rusa wani babban kurkukun da 'yan ta'addan Boko Haram ke tsare wadanda suka kama a cikin daji.

Masana tsaro sun bayyana cewa nasarar da sojoji suka samu na nuna irin yadda ake cigaba da ruguza 'yan ta'adda da rage musu karfi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng