"Ba a Nemi Izini ba": An Rufe Islamiyyar da Sarki Aminu Ado Bayero Ya Je Saukar Kur'ani

"Ba a Nemi Izini ba": An Rufe Islamiyyar da Sarki Aminu Ado Bayero Ya Je Saukar Kur'ani

  • Hukumar karamar hukumar Ilimi ta karamar hukumar Kumbotso a Kano ta dakatar da ayyukan makarantar Halqatul Mu’awiyya a Sabuwar Gandu
  • An ce an ɗauki matakin ne saboda zargin an shirya saukar Alƙur’ani ba tare da izini ba, tare da la’akari da yanayin tsari d ake ciki
  • Lamaarin na zuwa ne bayan makarantar ta gayyaci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya halarci taron saukar Al-Kur'ani mai tsarki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Kumbotso (LGEA), a jihar Kano, ta bayar da umarnin dakatar da dukkannin ayyukan makarantar Islamiyya ta Halqatul Mu’awiyya da ke unguwar Sabuwar Gandu.

Matakin ya biyo bayan shirye-shiryen makarantar na gudanar da saukar karatun Alƙur’ani Mai Girma da hukumar ta ce ana shirin yi ba tare da ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya dura Najeriya, zai je taro Gwamna Abba zuwa APC a Kano

An dakatar da ayyukan makarantar da ta gayyaci Sarki Aminu Ado Bayero sauka
H-D: Hon. Ghali Basaf, wasikar da ta dakatar da ayyukan makaranta, Sarki Aminu Ado Bayero Hoto: Abdullahi Ghali Basaf, Al Amin Abdullahi, Masarautar Kano
Source: Facebook

Freedom Radio ta wallafa a shafin Facebook ta wallafa cewa Shugaban karamar hukumar, Hon. Ghali Basaf ya bada umarnin dakatarwar a sanarwar da Sakataren Ilimi, Aminu Abdullahi ya sanya wa hannu.

An rufe Islamiyya a jihar Kano

A bidiyon da Dan Uwa Rano TV ya wallafa a shafin Facebook, an gano Sarki Aminu Ado Bayero na barin taron saukar da aka dakatar.

Sai dai sanarwar ta tabbatar da cewa wannan dakatar da gudanar da ayyuka da aka yi na wucin gadi ne.

Ta ce ba za a sake buɗe makarantar ba har sai an cika dukkannin sharuddan da hukumomi suka shimfiɗa, tare da samun sahalewar da ta dace.

Dalilan rufe islamiyya a Kano

A cewar bayanan da ke cikin takardar, makarantar ta shirya gudanar da taron saukar Al-ƙur’ani ne a daidai lokacin da ake fuskantar wasu ƙalubalen tsaro a yankin.

Hukumar ta ce wannan yanayi ya tilasta dakatar da taron, domin kauce wa duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta makiyayan da suka saki dabbobi a gonakin manoma

Karamar hukumar Kumbotso ta ce an rufe makarantar ne saboda tsaro
Taswirar jihar Kano da aka rufe wata Islamiyya saboda saukar Al-Kur'ani ba bisa ka'ida ba Hoto: Legt.ng
Source: Original

Hukumar LGEA ta kuma bayyana cewa matakin bai shafi ilimi ko addini kai tsaye ba, illa dai bin doka da oda.

Ta ƙara da cewa duk wata makaranta ko ƙungiya da ke shirin gudanar da taro mai ɗaukar jama’a dole ne ta nemi izini daga hukumomin da abin ya shafa.

Martanin jama'a kan rufe makaranta a Kano

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, na daga cikin manyan baƙin da aka gayyata domin halartar saukar karatun Alƙur’ani da aka shirya yi.

Tuni masu bibiyar shafukan sada zumunta suka mayar da martani game da dalilan da suka jawo aka dakatar da ayyukan makarantar.

Wani mai suna Hamisu Muhammad ya ce:

“Suna da damar gayyatar duk wanda suka ga dama, ba ra’ayin gayyatar tasa ne ya kamata ya zama matsala ba.”

Shi ma Umar Muhammad Umar ya bayyana cewa:

“Saboda shi yana APC, suma yanzu sun shiga APC, to za a yi kenan, muna jira.”

Kara karanta wannan

Makwabtan Fatima da aka kashe da yaranta 6 a Kano sun fusata rundunar 'yan sanda

Sarkin Kano ya koma makaranta

A baya, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya samu gurbin karatu a Jami’ar Northwest da ke Kano, domin ƙara zurfafa ilimi a fannin Shari’a.

A cikin wasiƙar, wadda ta fito daga Daraktan Jarrabawa, Shiga Jami’a da Rijista (DEAR) na Jami’ar Northwest, an tabbatar da cewa an bai wa Sarkin Kano gurbin karatun digirin LL.B

Matakin da Sarkin Kano ya ɗauka na komawa makaranta, duk da irin manyan digirori da yake da su, ya samu yabo daga jama’a da dama, inda suke ganin hakan a matsayin abin koyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng