Gwamna Ya Fadi Abin da Yake Kewa daga Osinbajo yayin Mulkinsu, Ya Soki Tinubu

Gwamna Ya Fadi Abin da Yake Kewa daga Osinbajo yayin Mulkinsu, Ya Soki Tinubu

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana kewar irin shugabancin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
  • Makinde ya ce abubuwa ba su daidai a gwamnatin yanzu, yana kwatanta saukin yanke shawara a zamanin Osinbajo
  • Gwamnan ya soki tsarin haraji na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana cewa ana kasa sauraron ra’ayin jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana game da jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Makinde ya ce yana kewar irin shugabancin da Farfesa Yemi Osinbajo, ya rika yi a lokacin yana rike da mukamin.

Gwamna ya tuna alherin Osinbajo lokacin mulkinsa da Buhari
Gwamna Seyi Makinde da Yemi Osinbajo. Hoto: Professor Yemi Osinbajo, Seyi Makinde.
Source: Facebook

Makinde ya yaba wa Yemi Osinbajo

Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin cikar Fasto Samson Ajetomobi, shekaru 60 a duniya, cewar TheCable.

An gudanar da biki ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. A wajen taron, Osinbajo ma ya halarta.

Kara karanta wannan

Badaru ya gana da Kwankwaso bayan ficewar Abba daga NNPP? An gano gaskiya

Makinde ya ce:

"Ranka ya dade, ni da kaina ina kewarka a wannan matsayi na mataimakin shugaban kasa.
“Mutane da dama ba su san dalilin da ya sa abubuwa ba su tafiya kamar da ba. Ba magana ta siyasa nake yi ba.”

Gwamnan ya tuna yadda Osinbajo ya taka rawa wajen hana shi kulle jihar Oyo gaba ɗaya a lokacin annobar COVID-19 a shekarar 2020.

Makinde ya bayyana cewa a wani taron majalisar tattalin arzikin kasa, an ba da shawarar a kulle dukkan jihohi, amma Osinbajo ya jagoranci yanke shawarar da ta bai wa Oyo damar kauce wa hakan.

Ya ce:

“A wancan lokaci, ban kai watanni bakwai a matsayin gwamna ba, kuma wannan shi ne aikina na farko a hidimar jama’a. Sai aka samu rikicin COVID-19 a kasar.
“Saboda wannan shawara tasa ne mutanen Oyo ba su shiga cikakken kulle-kulle ba a lokacin COVID."
Makinde ya soki salon mulkin Tinubu
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Makinde ya caccaki salon mulkin Tinubu

Sai dai gwamnan ya kwatanta wannan da halin da ake ciki a gwamnatin yanzu, musamman game da kudurin haraji na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Malami ya dauko da girma, ya hango masu daukar nauyin ta'addanci a kusa da Shugaba Tinubu

Ya ce duk da rokon a janye kudurin harajin domin a sake duba shi, ba a saurari kowa ba.

“Yanzu ba za ka iya fada wa mai iko gaskiya ba, duk da haka harajin zai ci gaba."

- Cewar Seyi Makinde

Makinde dai ya dade yana adawa da sauye-sauyen haraji na gwamnatin Tinubu tare da sukar wasu tsare-tsare na daban.

A watan Satumbar bara, ya ki sanya hannu kan kudurin bayan majalisar dokokin jiharsa ta amince da shi, yana cewa zai kara wa talakawa wahala a wannan lokaci mai tsananin matsin tattalin arziki, cewar Peopls Gazette.

Makinde ya magantu kan nasarar PDP

An ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi tsokaci kan masu ganin jam'iyyar PDP ta mutu murus a fagen siyasar Najeriya.

Seyi Makinde ya bayyana cewa jam'iyyar PDP na nan daram da karfinta kuma ba ta mutu ba kamar yadda wasu ke tunani.

Injiniya Makinde ya bayyana cewa jam'iyyyar PDP ta shirya ba mara da kunya a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.