Me Ya Rage wa Siyasar Kwankwaso bayan Ficewar Abba? An Sama Masa Mafita

Me Ya Rage wa Siyasar Kwankwaso bayan Ficewar Abba? An Sama Masa Mafita

  • An ji Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar NNPP sakamakon rikicin cikin gida, lamarin da ya girgiza tafiyar Kwankwasiyya
  • Masana siyasa sun ce ficewar gwamnan na iya janyo masa rasa manyan jiga-jigai da ’yan majalisa, wanda zai rage karfin NNPP da Kwankwasiyya
  • Makomar Kwankwasiyya yanzu na rataye ne kan irin matakin da Rabiu Musa Kwankwaso zai dauka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP a hukumance, jam’iyyar da aka zabe shi a karkashinta a zaben 2023.

Wannan mataki ya haifar da sabon rikici da tambayoyi kan makomar tafiyar Kwankwasiyya a Kano da Najeriya baki daya.

Abba ya raba gari da Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwasi da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Masana sun hango makomar Kwankwasiyya

Masana harkokin siyasa na ganin ficewar gwamnan na nufin raba gari da tafiyar Kwankwasiyya, tare da yiyuwar tafiya da manyan jami’an gwamnatinsa, cewar BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Tijjani Gandu ya yi wa Kwankwaso sabuwar waka Abba na fita daga NNPP

Wani masani kan al’amuran siyasa, Kabiru Sufi, ya bayyana cewa Kwankwasiyya ta yi babban rashi da ficewar gwamnan, inda ya ce NNPP ta rasa jiha guda daya da take alfahari da ita a matakin gwamnati.

Ya kara da cewa ba gwamna kadai ba ne zai iya barin jam’iyyar, domin akwai yiwuwar muqarrabansa da dama, ciki har da ’yan majalisar tarayya da na jiha, su bi shi.

Ya ce sanarwar da Kwankwaso ya yi na bai wa magoya baya damar bin gwamnati na iya haifar da rudani wajen tantance wadanda suka fice da gaske da kuma wadanda ke bin umarni ne kawai.

Ana hasashen makomar siyasar Kwankwasiyya
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

An shawarci Kwankwaso game da siyasarsa

Dangane da abin da ya kamata Rabiu Kwankwaso ya yi, masanin ya ce makomar tafiyar za ta dogara ne kan irin matakin da jagororinta za su dauka, musamman gaggauta fito da sabon shugabanci da tsari domin ci gaba da tafiyar.

A halin yanzu dai, ficewar Abba Kabir Yusuf daga NNPP ta kara tayar da kura a siyasar Kano, inda ake ganin magoya baya sun kasu kashi biyu – masu bin gwamna da kuma masu bin Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Abba ya rike akidar Kwankwasiyya gam duk da rabuwar da jam'iyyar NNPP

Wannan rikici ya sa makomar jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya ke ci gaba da zama cikin tambaya.

Abba Kabir Yusuf, wanda yake daga cikin manyan jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa, ya ce ya dauki matakin ficewa daga NNPP ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar.

Sai dai Sufi ya ce Kwankwasiyya an santa da jajircewa da juriyar hamayya, amma duk da haka, rasa masu rike da mulki na iya rage mata tasiri idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba.

An bukaci Kwankwaso ya hade da Barau

Mun ba ku labarin cewa masoyin jam’iyyar APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya ce fitar Abba Kabir Yusuf daga NNPP babban cin amana ne.

Kwamanda ya bayyana cewa sun riga sun dauki Sanata Barau Jibrin a matsayin dan takara a Kano, yana mai cewa hadin kan Barau da Kwankwaso zai iya kifar da Abba.

Dan Bilki ya ce tasirin Sanata Rabiu Kwankwaso a Kano bai gushe ba, yana mai jaddada cewa masu bin Abba suna bin bukatar kansu ne ba akida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.