Asiri Ya Tonu: An Yi Cushe a Sababbin Dokokin Harajin da Shugaba Tinubu Ya Kafa a Najeriya
- Kwamitin bincike da bangaren marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ya kafa ya gano wuraren da aka sauya a sababbin dokokin haraji
- An dai fara ce-ce-ku-ce kan zargin yin cushe a dokar haraji ne bayan wani dan Majalisa ya gabatar da korafi a gaban Majalisar wakilai
- Wannan ya sa bangaren marasa rinjaye ya lashi takobin gano gaskiya kan lamarin, kuma a yanzu ya fara sakin rahoton abubuwan da ya gano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Bangaren marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ya tabbatar da cewa an sauya sababbin dokokin harajin Najeriya da suka fara aiki a 2026.
'Yan Majalisar sun bayyana cewa an yi cushen ne bayan da Majalisar Tarayya ta riga ta amince da su, sannan kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma ya sanya musu hannu.

Kara karanta wannan
Malami ya dauko da girma, ya hango masu daukar nauyin ta'addanci a kusa da Shugaba Tinubu

Source: Facebook
Daily Trust ta ce wannan bayanin ya fito ne a cikin rahoton wucin gadi na kwamitin bincike na musamman da bangaren marasa rinjaye ya kafa don bincikar zargin cushen.
Wannan ka-ce-na-ce ya zo ne bayan dan majalisar wakilai, Hon. Abdulsamad Dasuki (PDP, Sokoto), ya tada maganar a zauren majalisa kan zargin bambanci tsakanin dokokin da ake yadawa da kuma wadanda majalisar ta amince da su.
Yadda aka kafa kwamitin bincike
A ranar 28 ga Disamba, 2025, bangaren marasa rinjaye ya lashi takobin kare cin gashin kansa na majalisa, inda ya yi gargadin cewa ba za su bar duk wani yunkuri na kakaba wa 'yan Najeriya dokokin bogi ba.
Sakamakon haka, a ranar 2 ga Janairu, 2026, shugaban marasa rinjaye, Rt. Hon. Kingsley Chinda, ya kafa kwamitin bincike mai mambobi bakwai karkashin jagorancin Hon. Afam Victor Ogene.
Muhimman Abubuwan da aka jirkita
Binciken kwamitin ya gano cewa an samu akalla nau'i daban-daban guda uku na Dokar Gudanar da Haraji da ake yadawa.
Ga wasu daga cikin manyan sauye-sauyen da aka gano wadanda ba su cikin abin da majalisa ta amince da shi:
- Rage Ma'aunin Biyan Haraji (Section 29(1)): An rage ma'aunin biyan haraji daga N50m zuwa N25m ga daidaikun mutane, sannan daga N250m zuwa N100m ga kamfanoni.
- Kai kara kotu (Section 41(8) & (9)): An shigar da wata doka da ke tilasta wa mai biyan haraji ya ajiye kashi 20% na kudin harajin da ake jayayya a kai kafin ya daukaka kara zuwa kotun haraji.
- Ikon Kwace Kadarori: Bangare na 64 ya ba hukumomin haraji ikon kama mutum da sayar da kadarori ba tare da izinin kotu ba
A rahoton Punch, kwamitin ya bayyana wadannan sauye-sauye a matsayin "rashin bin ka'ida da rashin mutunta doka."
Saboda haka, kwamitin ya bukaci a kara masa lokaci domin gudanar da bincike mai zurfi don gano wadanda ke da hannu a wannan zagon kasa ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

Source: Twitter
Oyedele ya yi bayani kan dokar haraji
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele ya yi karin haske kan sababbin dokokin haraji.

Kara karanta wannan
An fitar da sunayen mutane 177 da 'yan bindiga suka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna
Taiwo Oyedele ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sababbin dokokin ba za su janyo cire kudi kai tsaye daga asusun banki ba, komai girman kudin da aka tura.
Oyedele ya jaddada cewa galibi dokar haraji na shafar masu samun kudaden shiga masu yawa, ba kananan masu amfani da asusun banki ba.
Asali: Legit.ng
