Wutar Lantarkin Najeriya Ta Samu Babbar Matsala Ta Farko a 2026

Wutar Lantarkin Najeriya Ta Samu Babbar Matsala Ta Farko a 2026

  • Babban tushen samar da wutar lantarki a Najeriya ya durkushe, lamarin da ya jefa 'yan kasa a cikin duhu yau Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2026
  • Rahotanni sun nuna cewa zuwa karfe 1:00 na rana, babu wani kamfanin raba wuta da ya mu ko digo daga babban tushen samar da wuta na kasa
  • Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan matsala a 2026, duk da dai an sha fama da lalacewar wuta a shekarar da ta gabata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban tushen wutar lantarki na Najeriya gaba daya ya samu matsala a yau Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2025.

Wannan dai shi ne karo na farko da wutar lantarkin Najeriya ta lalace a sabuwar shekarar da aka shiga watau 2026.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi halin da yake ciki kan gudanar da mulkin Najeriya

Babban layin wutar lantarki.
Allon sanarwa da ke kusa da babban tushen wuta na Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Samar da wutar lantarki ya tsaya cik

Jaridar The Cable ta tattaro cewa a bisa ga bayanai da aka samo daga Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Najeriya (NISO), karfin samar da wutar ya fadi zuwa sifili (0 MW).

Bayanai daga NISO sun nuna cewa raba wutar lantarki ga kamfanonin rarraba wuta guda 11 (DisCos) ya tsaya cak zuwa karfe 1:00 na rana a yau Juma’a.

Dukkan kamfanonin rarraba wutar, wadanda suka hada da na Benin, Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano, Port Harcourt, Ibadan, Abuja, da Yola, ba su samu ko digon wuta ba.

Tarihin durkushewar tushen wutar Najeriya

A shekarar 2025, babban tushen samar da wutar lantarkin na kasa ya durkushe sau da dama, inda aka samu na karshe a ranar 29 ga watan Disamba, 2025.

Wadannan matsaloli na faruwa ne duk da kokarin inganta tsarin da nufin kara karfin wuraren samar da wutar da gwamnatin tarayya take yawan ikirarin tana y, in ji Vanguard.

Kara karanta wannan

APC: Gwamna Abba ya saka rana, zai tattara ya bar Kwankwaso a jam'iyyar NNPP

Matakan gyara wuta da aka dauka

Kamfanin samar da wuta na Niger Delta Power Holding Company (NDPHC) ya taba bayyana cewa ya maido da karin megawatt 450 ga babbar tashar wuta bayan kammala gyaran da aka yi wa tashar wutar lantarki ta Geregu NIPP.

Haka kuma, a ranar 9 ga Nuwamba, 2025, hukumar NISO ta sanar da cewa ta hada gwiwa da cibiyar hadin kai ta West African Power Pool (WAPP-ICC) domin gwada yadda za a hada tushen wutar Najeriya da na sauran kasashen yammacin Afirka.

Wutar lantarki.
Daya daga cikin manyan layukan wutar lantarki a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai duk da wadannan matakai da hukumomi ke dauka, har yanzu ana ci gaba da samun matsalar lalacewar tushen samar da wuta, wanda ke jefa yan Najeriya cikin duhu.

Najeriya na bin kasashe 3 bashin kudin wuta

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NERC ta ce kasashen Togo, Nijar da Benin ba su biya cikakken kudin wutar lantarki da suka sha daga Najeriya ba a zango na uku na 2025.

Kara karanta wannan

APC ta gaji da jiran Abba ya sauya sheka, an fara yi wa jama'a rajista

Wannan bashi ya samo asali ne daga wutar lantarki da Najeriya ke samarwa tare da sayarwa ga wadannan kasashe bisa yarjejeniyar da suka yi.

Hukumar ta bayyana cewa baya ga bashin da ya samo asali a zango na uku na 2025, akwai kuma tsofaffin basussuka daga zangunan baya da suka kai Dala miliyan 14.7.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262