Tinubu Ya Soke Tura Tsohon Gwamnan Kebbi Jakada zuwa Turkiyya Sa'o'i da Nada Shi

Tinubu Ya Soke Tura Tsohon Gwamnan Kebbi Jakada zuwa Turkiyya Sa'o'i da Nada Shi

  • Fadar shugaban kasa ta janye nadin tsohon gwamnan Kebbi, Usman Dakingari, a matsayin jakadan Najeriya zuwa Turkiyya bayan kasa da sa'o'i 24
  • Sanarwar janyewar ta zo ne yayin da aka tabbatar da nadin wasu manyan mutane uku a matsayin jakadu zuwa kasashen Amurka, Faransa da Birtaniya
  • Gwamnati ba ta bayyana dalilin janye nadin Dakingari ba, lamarin da ya haifar da tambayoyi a fagen diflomasiyyar Najeriya da kasar Turkiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fadar shugaban kasa ta janye nadin tsohon gwamnan Jihar Kebbi, Usman Dakingari, a matsayin jakadan Najeriya da ake shirin turawa Turkiyya, jim kadan bayan sanar da jerin sababbin jakadu.

Wannan mataki ya biyo bayan wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, inda ta bayyana amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nadin jakadu hudu daga cikin sama da mutane 60 da Majalisar Dattawa ta tantance.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tura jakadu zuwa Amurka da wasu kasashen Turai 3

Usman Dakingari, Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Tsohon gwamna Usman Dakingari da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Ahmad Usman
Source: Facebook

Sai dai a wata sanarwa da hadimin Tinubu, Sunday Dare ya fitar a kafar X, an bayyana cewa babu wani jakada da aka nada zuwa Turkiyya a halin yanzu.

Yadda aka sanar da nadin jakadu

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya fara bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Kayode Are a matsayin jakadan Najeriya zuwa Amurka.

Sanarwar ta kuma bayyana nadin tsohon shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa, NIA, Ayodele Oke a matsayin jakada zuwa Faransa.

Haka kuma, Amin Dalhatu, wanda ya taba zama jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, an sanar da nadinsa a matsayin jakada zuwa Birtaniya.

A cikin jerin sunayen, an bayyana Usman Dakingari a matsayin jakadan da aka tanada turawa Turkiyya, nadin da ya zo a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke shirin zuwa kasar Turkiyya a mako mai zuwa.

Bola Tinubu ya janye tura jakada Turkiyya

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa babban sansanin Boko Haram, sun bankado kabarin 'yan ta'adda

Sai dai a cikin sabon bayani daga fadar shugaban kasa, an janye magana kan Dakingari gaba daya, inda aka bayyana cewa ba a nada wani jakada zuwa Turkiyya ba.

Sanarwar ta sake jaddada nadin Are, Oke da Dalhatu, amma ta cire sunan Dakingari daga cikin jerin jakadun da aka amince da su.

Fadar shugaban kasa ba ta bayar da wani bayani kan dalilin da ya sa aka janye nadin tsohon gwamnan Kebbi ba, lamarin da ya bar jama’a da masu bibiyar al’amuran diflomasiyya cikin mamaki.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Matakin da Tinubu ya dauka kan jakadu

A cewar Onanuga, Shugaba Bola Tinubu ya riga ya rubuta takardar sanarwa zuwa ma’aikatar harkokin wajen Najeriya domin sanar da gwamnatocin kasashen Amurka, Faransa da Birtaniya game da jakadun da aka tanada musu.

The Cable ta ce ya ce wannan mataki ya bi ka’idojin diflomasiyya da ke bukatar sanar da kasashen da abin ya shafa kafin jakadu su fara aiki a hukumance.

Tinubu ya amince da hako mai a Ogun

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Ogun ya sanar da cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da aikin hako mai a jihar.

Kara karanta wannan

An bada umarnin kama tsohon hadimin gwamna da mutum 4 kan zargin alaka Bello Turji

Gwamna Dapo Abiodun ya sanar da haka ne yayin ganawa da wasu manyan kwamandojin sojojin ruwan Najeriya da suka ziyarce shi.

Baya ga hako mai, gwamnan ya sanar da cewa shugaban kasa ya ba jihar damar fara aikin babbar tashar jirgin ruwa da aka dade ana nema.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng