Tinubu Ya Tura Jakadu zuwa Amurka da Wasu Kasashe 3 Na Turai

Tinubu Ya Tura Jakadu zuwa Amurka da Wasu Kasashe 3 Na Turai

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara tura jakadu zuwa kasashen waje domin wakiltar Najeriya ta fuskar diflomasiyya
  • Mai girma Bola Tinubu ya tura hudu daga cikin jakadu 68 da majalisar dattawan Najeriya ta amince da su a watan Disamban 2025
  • Daga cikin jakadun da Shugaba Tinubu ya tura akwai, Ambassada Ayodele Oke, wanda zai wakilci Najeriya a kasar Faransa

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura jakadu huɗu daga cikin 68 da majalisar dattawa ta tantancesu.

Majalisar dattawa dai ta tantance jakadun a watan Disamban shekarar 2025 da ta gabata.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sace masu ibada a Kaduna, ya fadi kuskuren gwamnati

Shugaba Tinubu ya tura jakadu zuwa kasashen waje
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026.

Tinubu ya tura jakadu zuwa kasashen waje

A cewar sanarwar shugaban kasar ya amince da tura a Kanar Lateef Are a matsayin jakadan Najeriya zuwa Amurka.

“Shugaba Tinubu ya amince da tura Ambasada Ayodele Oke a matsayin jakadan Najeriya zuwa Faransa, da kuma Kanar Lateef Are a matsayin jakadan kasa zuwa Amurka.”

Kara karanta wannan

An bada umarnin kama tsohon hadimin gwamna da mutum 4 kan zargin alaka Bello Turji

“Haka kuma, shugaban kasa ya amince da tura Ambasada Aminu Dalhatu, tsohon jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, a matsayin Babban Kwamishinan Najeriya zuwa Birtaniya.”
“Sannan an tura tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Isa Dakingari Suleiman, a matsayin jakadan kasa zuwa Turkiyya, inda Shugaba Tinubu ke shirin kai ziyara ta musamman a mako mai zuwa.”
"A cikin wata takarda da shugaban kasa ya aikawa ma’aikatar harkokin waje, ya umarci ma’aikatar da ta sanar da gwamnatocin ƙasashen huɗu game da jakadun da aka tura, kamar yadda dokokin huldar diflomasiyya da suka tanada."

- Bayo Onanuga

Majalisa ta tantance jakadu

Ayodele Oke, Lateef Are da Aminu Dalhatu an tabbatar da su a matsayin jakadu a watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Alfarmar da Gwamna Abba Kabir ya nema yayin ganawa da Tinubu a Abuja

Tinubu ya tura jakada zuwa kasar Amurka
Mai girma Bola Tinubu da ke shugabantar Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Su ukun ne suka kasance rukuni na farko na sunayen jakadu da Shugaba Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa a watan Nuwamban 2025, bayan kusan shekara biyu babu jakadu a ofisoshin jakadanci na Najeriya.

A wannan watan na Nuwamba ɗin, shugaban kasa ya kuma tura sunayen karin jakadu 32 zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa da su.

Daga cikin waɗanda aka miƙa sunayensu akwai:

Reno Omokri, tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara, tsohon shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, tsohon Ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da tsohuwar uwargidan gwamnan Oyo, Fatima Florence Ajimobi.

Tinubu ya gana da Gwamna Makinde

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya labule da gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde.

Rahotanni sun nuna cewa daga zuwan Gwamna Makinde na PDP, ya wuce kai tsaye ya shiga ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ganawar ta su dai na zuwa ne yayin wasu ke fargabar cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da jawo 'yan adawa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng