Babbar Magana: Bayan Hari a Coci, Amurka Ta kuma Jan Kunnen Najeriya

Babbar Magana: Bayan Hari a Coci, Amurka Ta kuma Jan Kunnen Najeriya

  • Amurka ta buƙaci Najeriya ta ƙara tsaurara matakan kare Kiristoci bayan sace-sace a coci da aka yi a Kaduna
  • Gwamnatin Amurka ta yaba da nasarar kubutar da Kiristoci a Kwara da wasu makarantu, amma ta nuna damuwa kan sabbabin hare-hare
  • Nuhu Ribadu ya ce hare-haren addini barazana ne ga ƙasar baki ɗaya, yana mai cewa Bola Tinubu yana kokari a yankuna masu haɗari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Amurka ta yi magana bayan harin da yan bindiga suka kai a jihar Kaduna da sace masu bauta a coci.

Kasar Amurka ta buƙaci Najeriya da ta ɗauki ƙarin matakai masu ƙarfi da gaggawa domin kare al’ummomin Kiristoci, musamman bayan sace-sacen jama’a da aka yi a wasu coci a jihar Kaduna.

Amurka ta shawarci Najeriya bayan hari a cocin Kaduna
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Amurka, Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Amurka ta yabi Najeriya a wani bangare

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sace masu ibada a Kaduna, ya fadi kuskuren gwamnati

Karamar ministan harkokin siyasa na Amurka, Allison Hooker ta yi wannan kira ne a yayin wani taron babban kwamitin haɗin gwiwar Amurka da Najeriya a Abuja, cewar TheCable.

Hooker ta ce taron ya mayar da hankali ne kan yadda ƙasashen biyu za su haɗa kai domin dakile hare-hare kan Kiristoci, ba da fifiko ga yaƙi da ta’addanci da matsalar tsaro, binciken hare-hare, da kuma tabbatar da hukunta masu aikata laifuka.

Ta bayyana cewa duk da an samu ɗan ci gaba a ‘yan watannin baya, hare-haren da suka faru kwanan nan sun nuna cewa Najeriya na buƙatar yin ƙarin ƙoƙari domin tabbatar da tsaron Kiristoci da ‘yancinsu na yin addininsu.

A cewar Hooker, gwamnatin Najeriya ta samu nasarar kubutar da Kiristoci 38 da aka sace daga wani coci a jihar Kwara, da kuma mutane 265 da aka sace daga makarantar St. Mary’s Catholic.

“Wannan ci gaba ne na gaske, kuma sakamakon hulɗar da muke da ita da gwamnatin Najeriya kai tsaye.”
Amurka ta ji haushin sace Kiristoci a cocin Kaduna
Shugaba Donald Trump yayin taro a fadar White House. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Korafin Amurka kan sace Kiristoci a Kaduna

Sai dai ta nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun sace fiye da Kiristoci 170 a jihar Kaduna a ranar 18 ga Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya tsorata da barazanar kashe shi, ya yi alwashin shafe Iran a duniya

“Dole ne gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙaimi wajen kare Kiristoci da ‘yancinsu na yin addini cikin kwanciyar hankali."

- Allison Hooker

Martanin Ribadu ga bukatar Amurka

A nasa martanin, Nuhu Ribadu ya amince cewa matsalolin tsaro suna da girma, yana mai cewa gwamnati na ƙara ƙaimi a ayyukan soja da jami’an tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Ribadu ya jaddada cewa hare-haren da ake dangantawa da addini ba za a amince da su ba, kuma za a fuskance su da ƙarfi da adalci, cewar Vanguard.

Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kokari bangaren tsaro a wasu yankuna masu haɗari, tare da umarnin ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwar jami’an tsaro.

Amurka ta jajanta bayan rasuwar malamin Musulunci

Mun ba ku labarin cewa ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yi jimamin rasuwar malamin Musulunci da ya rasu a jihar Plateau.

An tabbatar da rasuwar Imam Abdullahi Abubakar, Malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci 300 a rikicin Plateau da ya faru a 2018.

Marigayi Imam Abdullahi ya shahara a duniya saboda jajircewarsa wajen kare rayuka ba tare da la’akari da addini ba a hare-haren 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.