Bayan Fara Gutsiri Tsoma, Sanusi II Ya Fadi Dalilin Komawa Jami'a Duk da Yana da PhD

Bayan Fara Gutsiri Tsoma, Sanusi II Ya Fadi Dalilin Komawa Jami'a Duk da Yana da PhD

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi rajista a jami'ar Northwest domin yin karatun digiri a fannin shari'a
  • Muhammadu Sanusi II ya yi tsokaci kan dalilin da ya sa ya koma aji domin sake samun kwalin digiri duk da yana da wasu
  • Sarkin ya bayyana cewa yana kasancewa cikin farin ciki a duk lokacin da ya samu kansa yana karatu ko koyarwa

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan shawarar da ya yanke ta komawa jami'a domin yin karatu.

Sanusi II ya bayyana cewa shawarar da ya yanke ta yin rajista a fannin karatun shari'a a jami’ar Northwest, Kano, cikar wani tsohon buri ne da yake da shi tun da dadewa.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya koma karatu a jami'a
Muhammadu Sanusi II na daukar lakca a jam'iar Northwest Hoto: Saifullahi Ahs.
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Sanusi II ya bayyana hakan ne bayan halartar darasi a jami’ar a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana

Meyasa Sanusi II ya koma aji?

Sanusi II ya ce duk da cewa yana da manyan digiri har da digirin digirgir (PhD), burinsa tun farko shi ne ya karanci fannin shari’a.

Ya bayyana cewa wannan shi ne digirinsa na farko na uku, bayan da ya taba karatu a fannin tattalin arziki a jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, sannan ya yi wasu karin karatuttuka a baya.

“Na sha fada cewa aji shi ne wurina na asali. Na kan yi farin ciki idan ina karatu ko koyarwa. Wannan babbar dama ce a gare ni na karanci fannin da na dade ina sha’awa."
"Doka tana ko’ina a rayuwarmu, tana tafiyar da iyalai, kwangila, dukiya, gado, har ma da yadda muke tuki a hanya. Ita ce kariyar da ke tabbatar da zaman lafiya da daidaito a al’umma."

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya fadi muhimmancin doka

Sarki Sanusi ya karyata rade-radin da ke cewa fara karatu a fannin shari'a, yana da alaka da shari’o’in da ya taba fuskanta a baya, yana mai cewa sha’awarsa kan doka ta ilimi ce da fahimta, ba saboda wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Hotunan Sarkin Kano Sanusi II bayan ya koma jami'a, ya shiga lacca da dalibai a aji

“Fahimtar doka na taimakawa sosai, amma sama da haka, doka ita ce ke rike al’umma wuri guda. Ranar da aka rasa doka da oda, masu karfi za su yi abin da suka ga dama, masu rauni kuma su sha wahala."

- Muhammadu Sanusi II

Dalilin Sanusi na zabar Northwest

Game da dalilin da ya sa ya zabi jami’ar Northwest, Sarkin ya ce jami’ar ce ta ba shi gurbin karatu, kuma kasancewarta ta jihar Kano ce, ya ga ya dace ya mara mata baya.

“Sau da yawa muna raina malamai da jami’o’inmu, alhali sun kai matakan ilimi irin na kasashen waje. Idan za ka karanci doka, ya dace ka karance ta a Najeriya. Me ya sa za ka karanci dokar Birtaniya alhali ba za ka zauna a can ba?”

- Muhammadu Sanusi II

Muhammadu Sanusi II ya koma karatu a jami'ar Northwest
Muhammadu Sanusi a dakin daukar karatu na jam'ar Northwest Hoto: Saifullahi Ahs.
Source: Facebook

Ya batun sarautar Kano?

Dangane da yadda zai hada nauyin sarauta da karatu lokaci guda, Sarkin ya ce:

“Ina zama dalibi da safe, Sarkin Kano da rana. Talata, Laraba da Alhamis ranakun darasi ne, yayin da Litinin da Juma’a nake zaman fada kamar yadda aka saba."
"Idan ban samu damar zuwa aji ba, zan shiga ta yanar gizo na saurara. Jami’ar ta sassauta mini wajen daidaita jadawalin karatuna."

Kara karanta wannan

Abin da gwamnati da 'yan sanda suka ce kan batun sace mutane sama da 100 a cocin Kaduna

Sanusi II ya ragargaji 'yan siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya koka kan halin 'yan siyasa a Najeriya.

Sanusi II ya ce ’yan siyasar Najeriya suna hana ci gaban kasa da gangan, domin suna daukar mukaman gwamnati a matsayin daga su sai iyalansu.

Sarkin ya bayyana cewa manyan ’yan siyasa sun kaurace wa damar habaka kasa saboda sun mayar da mukamin gwamnati na kansu, iyalansu da abokansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng