Kaduna: Gwamna Ya Sha Alwashi, Zai Ceto Mutum Sama da 170 da 'Yan Ta'adda Suka Sace

Kaduna: Gwamna Ya Sha Alwashi, Zai Ceto Mutum Sama da 170 da 'Yan Ta'adda Suka Sace

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ziyarci Kurmin Wali bayan harin ‘yan bindiga, inda suka bi coci-coci tare da dauke mutane sama da 100
  • A ziyarar, Gwamnan ya bayyana harin da aka kai wa coci-coci uku a ranar 18 ga Janairu, 2026 a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba
  • Gwamnatin Kaduna ta dauki alkawarin hada kai da sojoji da sauran hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankunan jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya kai ziyara kauyen Kurmin Wali da ke Karamar Hukumar Kajuru, inda aka kai wani mummunan hari na ‘yan bindiga a kwanakin baya.

A ziyarar da ya kai a ranar Laraba, 21 ga watan Janairu, Uba Sani iya jajanta wa al’ummar yankin tare da duba halin da ake ciki bayan harin da ya janyo asarar rayuka da kuma sace mutane.

Kara karanta wannan

APC ta gaji da jiran Abba ya sauya sheka, an fara yi wa jama'a rajista

Uba Sani ya ziyarci kauyen da yan bindiga suka kai wa hari
Gwamna Uba Sani tare da wasu daga cikin iyalan wadanda aka sace a Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafin Facebook na Gwamnan, Uba Sani ya amince da faruwar lamarin tare da bayyana cewa harin da aka kai a ranar 18 ga Janairu, 2026 abin bakin ciki ne matuka.

Gwamnan Kaduna ya ziyarci kauyen Kurmin Wali

A sakon, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ba za a ci gaba da lamuntar irin wannan mugun aiki ba. Ya ce irin wannan hari ya sabawa duk wata ka’ida ta zaman lafiya da mutunta rayuwar dan Adam.

Gwamna Uba Sani ya jajanta wa wadanda abin ya shafa da iyalansu, yana mai tabbatar masu da cewa gwamnatinsa ba za ta yi shiru ba kan lamarin.

Uba Sani ya yi alkawarin ceto mutanen da aka sace a Kaduna
Gwamna Uba Sani a lokacin da ya ke jawabi ga iyalan mutanen da aka sace a Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kara kaimi wajen daukar matakan tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin da ma jihar baki daya.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki kafada da kafada da sojoji da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin tabbatar da dawowar dukkannin mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya yi magana game da makamai da DSS ta gano a 'gidansa' na Kebbi

Kiran Gwamnan Kaduna ga Ministan tsaro

Gwamna Uba Sani ya yi kira ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, da ya taimaka wajen kafa sansanin soji a yankin Kurmin Wali domin kara tsaro da dakile ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagu.

Baya ga batun tsaro, gwamnan ya sanar da shirye-shiryen gina hanyar shiga kauyen Kurmin Wali, kafa cibiyar kula da lafiya ta matakin farko, da samar da wasu muhimman kayayyakin more rayuwa.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida na cikin gida da na kasa da kasa da suka raka shi, Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na da cikakken kudurin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kaduna.

'Yan sandan Kaduna sun tabbatar da sace mutane

A baya, mun ruwaito cewa Rundunar yan sandan kasa ta tabbatar da cewa an sace Kiristoci sama da 100 a kauyen Kurmin Wali, da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, bayan harin ‘yan bindiga a yankin.

Kara karanta wannan

Kujerar Hajji, sabon gida da wasu kyaututtuka 3 da Gwamna Abba ya yi waijin Fatima

Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce an yi garkuwa da mutane masu tarin yawa, amma ta musanta ikirarin da ke cewa an sace mutanen ne kai tsaye daga wuraren ibadarsu.

A cewar rundunar, kalaman Kwamishinan ‘Yan Sanda ba wai musanta aukuwar harin ko sace mutanen ba ne, illa dai amsa ce da aka bayar a lokacin da ake jiran cikakken rahoto daga jami’an da ke bakin aiki a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng