Duhu Ya Lullube Kano yayin da Ma'aikatan KEDCO Suka Tsunduma Yajin Aiki
- Ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO sun shiga yajin aikin sai baba ta gani, lamarin da ya jefa Kano da kewaye cikin matsanancin duhu
- Kungiyoyin ma’aikata sun ce sun dauki matakin ne bayan wa’adin da suka bai wa shugabancin kamfanin ya cika ba tare da cimma wata matsaya ba
- Sai dai shugabancin KEDCO ya ce korafe-korafen sun shafi tsofaffin batutuwa ne, yana mai cewa ana ci gaba da daukar matakai kan jin dadin ma’aikata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Al’ummar birnin Kano da wasu yankuna na kewaye sun fada cikin duhu bayan da ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO, suka fara yajin aiki.
Sun ce yajin aikin ya biyo bayan gazawar shugabancin kamfanin na cika bukatun ma’aikata bayan karewar wa’adi da aka sanya musu.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa kungiyoyin ma’aikata sun bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu ta jima, abin da ya sa suka yanke shawarar tsaurara matakai.
Dalilan shiga yajin aikin ma'aikatan KEDCO
Kungiyar manyan ma'aikatan rarraba wuta ta SSAEAC ta ce sun shiga yajin aikin ne a Kano sakamakon abin da suka kira munanan yanayin aiki.
Mataimakin shugaban kungiyar SSAEAC na Arewa, Rilwan Shehu, ya ce sun yi zanga-zanga zuwa ofishin KEDCO ne domin dakatar da ayyuka saboda rashin cika yarjejeniyoyi.
A cewarsa, tun daga shekarar 2014 ake fama da matsaloli da suka hada da rashin tura kudin fansho, rashin biyan hakkoki bayan mutuwa da kuma yanayin aiki mara kyau.
Zarge-zargen nuna wariya a kamfanin KEDCO
Shima mataimakin shugaban kungiyar NUEE na Arewa maso Yamma, Ado Gaya, ya yi zargin cewa shugabancin KEDCO na nuna wariya wajen karin girma.
Ya ce akwai ma’aikata da suka shafe sama da shekaru 10 ba tare da samun karin matsayi ba, duk da kwarewa da dadewar aiki.
A cewarsa, karin girman da aka yi kwanan nan ya fifita wasu ‘yan tsiraru ne bisa muradin kashin kai, ba bisa ka’idar aiki ba.
Tasirin yajin aiki KEDCO a Kano
Bayan fara yajin aikin, wutar lantarki ta dauke a sassa da dama na birnin Kano da yankunan makwabta, lamarin ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci, masana’antu da ayyukan yau da kullum na jama’a.
Wasu mazauna birnin sun bayyana damuwa kan yadda tsawon yajin aikin zai iya jawo kara tabarbarewar tattalin arziki da rayuwar jama’a.

Source: UGC
Martanin shugabancin KEDCO a Kano
A wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, ya fitar a ranar Laraba, kamfanin ya musanta zarge-zargen ma’aikata.
Sanarwar da ya fitar a Facebook ta ce tun bayan karbar mukami watanni bakwai da suka gabata, an mayar da hankali kan jin dadin ma’aikata da hakkokinsu.
Ta kara da cewa an biya sama da kashi 80 cikin 100 na kudin fansho na shekarar 2025 da aka amince da su kuma an bi ka'ida wajen karin matsayi.

Kara karanta wannan
Mutanen Dorayi sun fadi ainihin abin da ya faru kan kisan Fatima da yaranta 6 a Kano
Najeriya na bin bashin kudin wuta
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar lantarki ta NERC a Najeriya ta ce tana bin wasu kasashen Yammacin Afrika bashin kudin wuta.
A bisa sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce kasashen da suka gaza biyan cikakken kudin wutar da suka sha a 2025 su ne Nijar, Benin da Togo.
Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar NERC ta bayyana cewa idan aka tattara kudin da ta ke bin kasashen sun kai Naira biliyan 25.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

