Abubakar Malami Ya Yi Magana game da Makamai da DSS Ta Gano a 'Gidansa' na Kebbi
- Tsohon Ministan Shari'a a Najeriya, Abubakar Malami ya musanta zarge-zargen ta’addanci da hukumar tsaro ta DSS ta danganta da shi
- Tsohon Ministan da ke tsare a hannun DSS, ya ce babu wata hujja kan zargin gano makamai a gidansa ko wuraren da ke da alaƙa da shi
- Ofishin Malami ya nuna damuwa kan tsare shi ba tare da samun damar ganin lauya ko iyali ba, yayin da ake ci gaba da karyata zargin da ake masa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon babban lauyan kasa (AGF) kuma tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya musanta zarge-zargen ta’addanci da aka jingina masa.
Haka kuma tsohon Ministan ya karyata ikirarin cewa an gano makamai a wani gida da ake alakanta shi da shi a birnin Kebbi da ke jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana

Source: Twitter
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin watsa labarai, Mohammed Doka, ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook.
Abubakar Malami ya karyata ikirarin DSS
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa sanarwar da ofishin tsohon AGF ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa wadannan zarge-zarge ƙarya ne kuma ba su da tushe a kowanne kundin hukuma.
Sanarwar ta ce Malami, wanda Babban Lauya ne a Najeriya (SAN) kuma a halin yanzu yana tsare a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS), ta ce babu wanda ya same shi da laifin da ake zargin ya aikata.
Ta zargi wasu sassan kafafen yada labarai da gabatar da zarge-zarge da bincike da ake ci gaba da yi a matsayin hujjar ya yi laifi, kuma ya saba da ka’idar kundin tsarin mulki.
Sanarwar ta kuma karyata rahotannin da ke cewa an gano tarin makamai ko harsasai a wata kadarar da ke da alaƙa da Malami, tana mai cewa babu wata sanarwa a kan wannan da aka isar wa iyalansa ko lauyoyinsa.
Malami ya yi watsi da zargin ta'addanci
Haka kuma, sanarwar da ofishin Malami ya fitar ta yi watsi da duk wani zargin da ke danganta shi da ta’addanci ko tallafa masa.
Ta kara da cewa an yi wadannan ikirari ba tare da ambaton wani mutum, kungiya, kwanan wata ko wata hujja da za ta tabbatar da cewa Malami ya yi laifin.
Ofishin yada labaran Malami ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare shi da SSS ke yi, yana mai cewa tun bayan kama shi a ranar Litinin, an hana shi ganin iyalansa, lauyoyinsa da abokan hulɗarsa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Malami babban jigo ne a jam’iyyar ADC, kuma ya bayyana a bainar jama’a aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a shekarar 2027.
Kotu ta karbe kadarorin Malami
A baya, mun wallafa cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaƙa da tsohon Antoni Janar na Tarayya (AGF) Abubakar Malami, SAN.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin, yayin da yake yanke hukunci kan wata buƙatar gaggawa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta shigar a gaban kotun.
A hukuncin, kotun ta amince da bukatar EFCC na ɗan lokaci, tare da bada umarnin a ƙwace kadarorin domin hana su salwanta ko canza mallaka har sai an kammala bincike da shari’ar da ke gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

