Gwamna Abba Ya Yi Alkawari kan Kisan Fatima da Yaranta 6, Hanifa da Masallata a Kano

Gwamna Abba Ya Yi Alkawari kan Kisan Fatima da Yaranta 6, Hanifa da Masallata a Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ta'aziyya ga mutumin da aka kashe matarsa da 'ya'yansa shida a unguwar Dorayi Chiranci
  • Abba ya sha alwashin cewa ba zai yi wata-wata ba wajen rattaba hannu kan takardar hukuncin kisa kan wadanda ake zargi idan kotu ta yanke hukunci
  • Ya kuma umarci kwamishinan shari'a na Kano, ya hanzarta kammala shari'ar domin duk mai hannu a lamarin ya fuskanci hukunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa zai sa hannu kan takardar hukuncin kisa ga duk wanda kotu ta kama da laifin kisan gillar da aka yi wa Fatima da yaranta shida.

Ya kuma sha alwashin sa hannu kan takardar hukuncin kisan wadanda suka kashe Hanifa da kuma wadanda suka banka wuta a masallacin Gezawa har mutane da dama suka kone.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta makiyayan da suka saki dabbobi a gonakin manoma

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi a wurin taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya dauki zafi kan kisan Fatima

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Gwamna Abba ya ce duk wanda kotu ta tabbatar ya aikata daya daga cikin wadannan munanan laifuffuka, zai rattaba hannu a zartar masa da hukunci.

Abba Gida-Gida ya yi wannan alkawari ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya da mutumin da aka kashe iyalansa a Dorayi Chiranchi da ke cikin jihar Kano.

Domin tabbatar da adalci, Gwamna Abbaa ya umarci Kwamishinan Shari’a da ya hanzarta shari’ar wadanda ake zargin da aka riga aka kama game da wadannan kashe-kashe.

Mai girma gwamnan ya ba da tabbacin cewa duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukunci yadda ya kamata.

Gwamna Abba ya yi alhinin kisan Fatima

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook ranar Laraba.

Gwamna Abba ya nuna matukar alhininsa kan wannan mummunan lamari, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin jiha za ta yi kokarin gyara rayuwar mahaifin da aka kashe wa iyali domin ya koma cikin hayyacinsa.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Sarki Sanusi II ya roki Abba ya yi ga makasa Fatima da 'ya'yanta 6

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da mutumin da aka kashe iyalansa gaba daya a Kano Hoto: Abba S. Malami
Source: Facebook

Gwamna Abba ya jinjina wa Rundunar ‘Yan Sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da sauran hukumomin tsaro kan hadin kan da suka nuna da kuma matakan gaggawa da suka dauka wajen kamo wadanda ake zargin.

Ya karkare da addu'ar Allah Madaukakin Sarki ya jikan mamatan, ya kuma ba wa iyalansu da mutanen Jihar Kano hakurin jure wannan babban rashi.

Yan sanda sun soki makwabtan Fatima

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Kano ta karyata zargin da makwabtan Fatima Abubakar ke yadawa a kafafen sada zumunta bayan sun gaza kai dauki har aka kashe ta da yaranta shida.

A wata sanarwa, kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana takaicinsa game da abin da ya kira “ƙarya” da makwabtan Fatima ke yadawa.

SP Abdullahi Kiyawa, ya zargi mutanen da nade hannaye, inda ya bayyana cewa babu wani agaji na gaske da suka kai wa matar da yaranta har aka kashe su duka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262