Kotu Ta Hukunta Makiyayan da Suka Saki Dabbobi a Gonakin Manoma

Kotu Ta Hukunta Makiyayan da Suka Saki Dabbobi a Gonakin Manoma

  • Wata kotu ta musamman a jihar Jigawa ta yanke hukunci kan wasu makiyaya da ake zargi da sakin dabbobinsu a gonakin manoma
  • Kotun ta samu makiyayan da laifuffuka a shari'ar wadda kwamishinan 'yan sanda na jihar Jigawa ya shigar a gabanta
  • Alkalin kotun ya umurci su biya diyya ta miliyoyin Naira tare da ba su wa'adin kwanakin da za su daukaka kara

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Wata kotu ta musamman kan rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa ta yanke hukunci kan shari'ar da aka shigar a gabanta.

Kotun ta umurci makiyaya tara da su biya diyya ta Naira miliyan 500 ga manoman da amfanin gonakinsu ya lalace a karamar hukumar Birnin Kudu.

Kotu ta hukunta makiyaya a Jigawa
Taswirar jihar Jigawa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar TheCable ta ce alkalin kotun, Yusuf Abubakar, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 20 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An bada umarnin kama tsohon hadimin gwamna da mutum 4 kan zargin alaka Bello Turji

Kotu ta samu makiyaya da laifi

Yusuf Abubakar ya jingina hukuncin da tanade-tanaden dokar 'Penal Code', ciki har da sashe na 78, 19 da 322.

Shari’ar wadda kwamishinan ‘yan sanda na jihar Jigawa ya shigar, ta shafi Ilu Adamu da wasu makiyaya takwas, kuma ta shafe fiye da shekaru biyu ana shari’a kafin yanke hukunci.

Rahoton Premium Times ya bayyana cewa an tuhumi wadanda ake zargin da laifuffuka hudu, ciki har da barin shanunsu su shiga gonakin noma ba bisa ka’ida ba.

Lamarin da ya jawo babbar asarar amfanin gona, wanda hakan ya saba wa sashe na 97 na 'Penal Code'.

Laifuffukan da aka samu makiyayan da su

A hukuncinsa, alkalin ya kuma dora laifi a kan wadanda ake tuhumar bisa lalata kadarorin shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN) na jihar Jigawa.

Kotu ta tabbatar da cewa makiyayan sun kona tayar tarakta da babur mallakar shugaban AFAN, inda ta umurce su da su biya Naira dubu 500 a matsayin diyya.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sanya Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC kafin zaben 2027'

Alkalin ya kara da cewa wadanda ake tuhumar sun ji wa wasu manoma rauni, abin da ya saba wa sashe na 332 da 114 na dokar Penal Code.

Bayan nazarin hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar, kotun ta samu makiyayan da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Kotu ta hukunta makiyaya a jihar Jigawa
Wani makiyayi na tsatsar nono a jikin saniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wane hukunci kotu ta yanke?

Sakamakon haka, kotun ta umurci wadanda aka samu da laifi da su biya Naira miliyan 500 a matsayin diyya ga manoman da abin ya shafa, tare da ba su wa’adin kwanaki 30 domin daukaka kara kan hukuncin.

Lamarin da ya kai ga wannan shari’a ya faru ne a dazuzzukan Kwarsa, Larau da Tukuda da ke karamar hukumar Birnin Kudu.

Wadannan yankuna sun dade suna fuskantar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya kan batun amfani da filaye da wuraren kiwo.

'Yan bindiga sun tarwatsa makiyaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare kan Fulani makiyaya a jihar Plateau.

Mummunan harin na 'yan bindiga ya haifar da sace shanu kimanin 168 tare da tarwatsa makiyayan da ke kiwo a yankunan da ke karamar hukumar Barikin Ladi.

Tsagerun yan bindigan sun afka wurin kiwo suna harbe-harbe, abin da ya tilasta makiyaya tserewa domin kare rayukansu, yayin da maharan suka tsere da dabbobin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng