An bada Umarnin Kama Tsohon Hadimin Gwamna da Mutum 4 kan Zargin Alaka da Bello Turji

An bada Umarnin Kama Tsohon Hadimin Gwamna da Mutum 4 kan Zargin Alaka da Bello Turji

  • Tsohon hadimin gwamnan Zamfara, Musa Kamarawa da wasu mutum hudu da gwamnatin tarayya ta maka a kotu sun jefa kansu a matsala
  • Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da umarnin kamo mutum biyar da ake tuhuma da taimakawa dabar Bello Turji
  • Hakan ya biyo bayan bukatar da lauyan gwamnatin tarayya ya gabatar a zaman kotun na yau Laraba, 21 ga watan Janairu, 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da sammacin kamo wasu mutane biyar da ake zargi da taimakawa shahararren jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji.

Alkalin kotun, Mai Shari'a Alkali Emeka Nwite ne ya ba da umarnin a ranar Laraba, bayan lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya shigar da bukatar hakan.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen mutane 177 da 'yan bindiga suka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna

Kotun tarayya.
Babban alon sanarwa da ke kusa da kotun tarayya a Abuja Hoto: Federal High Court
Source: Getty Images

Kotu ta bada umarnin kama Musa Kamarawa

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kotun ta amince da bukatar gwamnati ne sakamakon rashin bayyanar wadanda ake karar a gabanta domin fuskantar shari’arsu.

Wadanda ake zargin sun hada da Musa Kamarawa, wanda ya ayyana kansa da tsohon hadimin tsohon gwamnan Zamfara kuma karamin ministan tsaro na yanzu, Bello Matawalle.

Sauran mutane hudu su ne,Abubakar Hashimu (wanda aka sani da Doctor), Samuel Chinedu, da kuma Lucky Chukwuma, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Dalilin kotu na bada umarnin

Tun farko, Alkali Nwite ya tambayi lauyansu, A.M. Lukman, inda suke, sai ya amsa da cewa Musa Kamarawa ya tabbatar masa za su zo kotu, yana mai cewa shi kansa ya yi mamakin rashin ganinsu.

Sakamakon haka, Mai Shari'a Nwite ya amince da bukatar lauyan gwamnarin tarayya na ba da sammacin kamo wadanda ake karar a duk inda aka same su.

A ranar 16 ga Disamba, 2024, gwamnatin tarayya ta shigar da kara kan wadanda ake zargin, ciki har da Bello Turji, Aminu Muhammad, da Sani Lawal, wadanda aka ce har yanzu suna can daji.

Kara karanta wannan

Kotu ta bayar da belin kwamishinan da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci, ta gindaya sharudda

Zargin suna da alaka da Bello Turji

Ana zargin wadanda ake karan da samar da kayayyaki da makamai ga kungiyoyin 'yan ta'adda karkashin jagorancin Bello Turji, Kachalla Halilu, Danbokolo, Lawali, Atarwatse, Buderi, da sauransu.

Suna fuskantar tuhumar sayo da samar da kwayoyi ba bisa ka'ida ba, da suka hada da allurar penta da ganyen wiwi; kayan abinci; kakin sojoji da na 'yan sanda ga kungiyoyin ta'addancin.

Haka kuma, ana zarginsu da kai buhunan siminti, kwanon rufi, kusoshi, da sandunan karfe zuwa sansanonin 'yan ta'adda da ke cikin dazuzzukan jihohin Zamfara, Sokoto, da Kaduna.

Bello Turji.
Kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Najeriya, Bello Turji Hoto: Hasan Aminu
Source: Facebook

An bayyana cewa laifin ya saba wa Sashe na 17 na Dokar Hana Ta’addanci ta shekarar 2013, kuma hukunci na karkashin wannan sashe na dokar.

Bayan ba da umarnin kama mutanen a duk inda aka same su, alkalin ya sanya ranar 24 ga Fabrairu, 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Bello Turji ya yi barazana a Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji ya turo sako mai daga hankali ga mazauna Tidibale a karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Alfarmar da Gwamna Abba Kabir ya nema yayin ganawa da Tinubu a Abuja

Lamarin ya sake dawo da fargaba da zaman dar-dar a kauyen Tidibale, wani ƙaramin ƙauyen manoma da ke a Jihar Sakkwato.

An ce barazanar Turji ta sa iyalai da dama sun fara barin gidajensu da gonakinsu, suna tafiya zuwa wuraren da suka fi tsaro domin tsira da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262