Hukuncin da Sarki Sanusi II Ya Roki Abba Ya Yi ga Makasa Fatima da ’Ya’yanta 6
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi jimamin kisan gilla da aka yi wa wata mata da 'ya'yanta shida wanda ya tayar da hankali
- Basaraken ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya rattaba hannu kan hukuncin kisa ga masu laifin kisan kai
- Sarkin ya ce rashin aiwatar da hukuncin kisa na kara bai wa masu aikata kisan gilla kwarin gwiwar ci gaba da aikata laifuffuka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya roki Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya rattaba hannu kan hukuncin kisa kan masu laifin kisan kai.
Sarkin ya ce hakan ne ya kamata ga duk wadanda kotu ta same su da laifin kisan kai, yana mai cewa hakan zai zama darasi da gargadi ga sauran jama’a.

Source: Facebook
Rokon da Sanusi II ya yi ga Abba Kabir
Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake martani kan kisan gilla da aka yi wa wata mata mai suna Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida, cewar Vanguard.
Ya bayyana kisan a matsayin danyen aiki na rashin imani da tausayi, yana mai cewa hakan na nuna gazawar al’umma wajen aiwatar da adalci da hukuncin kisa kamar yadda doka ta tanada.
A cewarsa, ya kamata a yi gaggawar gurfanar da wadanda aka kama bisa zargin aikata wannan kisan, kuma da zarar kotu ta yanke hukunci, gwamna ka da ya yi kasa a gwiwa wajen amincewa da aiwatar da hukuncin kisa.
Sarkin Kano ya ce:
“Muna mika ta’aziyyarmu ga mijin marigayiyar, iyalinta da daukacin al’ummar Kano, idan kasa na kyale mutane su kashe wasu ba tare da hukunci ba, kuma masu laifin na fita ba tare da fuskantar adalci ba.

Kara karanta wannan
Mutanen Dorayi sun fadi ainihin abin da ya faru kan kisan Fatima da yaranta 6 a Kano
“A wannan kasa, mutum zai kashe wani, ya amsa laifi a kotu, kotu ta yanke masa hukuncin kisa, amma ba a aiwatar da hukuncin saboda gwamna bai rattaba hannu ba, ba daidai ba ne a yi wa mai kisan kai afuwa saboda tausayi, domin shi bai tausaya wa wanda ya kashe ba.
“Ba kowa ne ke da ikon yafewa mai kisan kai ba, wannan hakki ne na iyalan wanda aka kashe da kuma Allah, ba na gwamnati ba.”
Sarkin ya jaddada cewa dakatar da aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya ya jawo yawaitar kisan kai, inda a wasu lokuta ma ake bai wa masu laifi afuwa.

Source: Facebook
Sarki Sanusi II ya yabawa dan sanda
Sanusi II ya ce bambanci ne idan laifin ya shafi satar kudi ko cin hanci, amma a batun kisan kai, dole ne adalci ya tabbata, cewar Leadership.
Sarkin ya ce idan mutane suka san cewa duk wanda ya kashe wani shi ma za a kashe shi, hakan zai zama babbar kariya daga aikata laifi.
Ya yabawa ’yan sanda bisa saurin kama wadanda ake zargi, tare da fatan kotu za ta hanzarta shari’ar kamar yadda Alkalin Alkalan Jiha zai bayar da umarni.
An biyawa Haruna Bashir kujerar Makkah
A baya, an ji cewa mutane na ci gaba da taya Malam Haruna Bashir jimami bayan iftila’in hallaka iyalinsa a Kano.
Lamarin ya jawo kokarin tara tallafi daga jama’a karkashin jagorancin lauya Abba Hikima wanda ya tabbatar wata Hajiya ta biya masa kujerar Hajji.
Abba Hikima ya ce ana ci gaba da karɓar gudunmawa, inda aka riga aka tara makudan kudi domin nuna masa kauna.
Asali: Legit.ng

