Sheikh Daurawa Ya Je Ta'aziyya ga Magidancin da Aka Kashewa Iyalai a Kano,Ya Yi Masa Nasiha

Sheikh Daurawa Ya Je Ta'aziyya ga Magidancin da Aka Kashewa Iyalai a Kano,Ya Yi Masa Nasiha

  • Ana ci gaba da alhini tare da jimamin danyen aikin da wasu matasa suka aikata kan iyalan wani bawan Allah a jihar Kano
  • Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya je ta'aziyya ga malam Haruna Bashir wanda aka kashewa mata da 'ya'yansa shida
  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi masa nasihohi tare da jajanta masa kan wannan rashin imanin da aka aikata masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya je ta'aziyya ga magidancin da wasu matasa suka hallaka masa iyalansa.

Sheikh Daurawa ya nuna alhininsa tare da jajantawa malam Haruna Bashir wanda matasan suka kashewa matarsa tare da 'ya'yanta guda shida.

Daurawa ya je ta'aziyya ga malam Haruna Bashir da aka kashewa iyalai a Kano
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa tare da Malam Haruna Bashir Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Malamin addinin Musuluncin ya sanya bidiyon jawabin da ya yi a wajen ta'aziyyar ne a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 20 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An biya wa mahaifin yara 6 da aka yi wa kisan gilla kujerar Makkah, ya samu kyauta

Daurawa ya girgiza kan kisan Fatima da yaranta

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa mummunan lamarin ya girgiza mutane matuka gaya saboda girman ta'addancin da aka aikata.

"Kowa ya san tashin hankali da al'umma Musulmi ba iya na wannan unguwa, ko na wannan jiha ko na wannan kasa suka shiga, kusan duk duniya wannan labarin ya girgiza mutane."
"Ya girgiza mutane saboda abu ne ba a taba ganin faruwar irinsa ba. An yi ta yin rashin imani daban-daban amma wannan rashin imanin ya bambanta da kowanne, shiyasa ya tayar da hankalin duniya."

- Sheikh Aminu Daurawa

Wace nasiha Daurawa ya yi masa?

Sheikh ya bayyana cewa lamarin ba shi kadai ya shafa ba, ya shafi dukkan al'umma ne domin kowa ya fito ya nuna alhininsa.

Ya yi masa nasiha da ya dauki hakuri da juriya tare mika lamarinsa ga ubangiji domin iyalan nasa sun samu mutuwa ta shahada.

Sheikh Daurawa ya tunatar da shi cewa idan Allah Ya ga dama yana iya sanyawa yaran da ya rasa su zama sanadiyyar shigarsa gidan Aljannah da samun rahama.

Kara karanta wannan

Albashi: Miliyoyin da Shugaban Ƙasa, Mataimaki da sauran jami'an gwamnati suke karba

"Malam Haruna Bashir wannan jarabawa ba kai kadai ta shafa ba, ka dai ga yadda suke ta cincirindo, suke ta nuna alhininsu kan wannan jarabawa da ta same ka, ta same mu baki daya."
"Muna fatan za ka maida al'amarinka zuwa ga Allah. Wannan iyali na ka sun yi shahada kuma muna fata yanzu haka suna cikin kyakkyawan sakamako."
"Ba ka yi asarar iyalinka ba, watakila ma idan Allah ya ga dama ya sa wadannan yara su zama dalilin shigarka Aljannah, samun rahamarka da jin kai a gareka."
"Saboda haka kar ka dora wani abu, ka ci gaba da hakuri, ka ci gaba da juriya."

- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Daurawa ya je ta'aziyya kan kisan da aka yi a Kano
Shugaban hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Daurawa ya kadu kan kisan Fatima da yaranta

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim, ya yi alhini kan kisan da aka yi wa wata matar aure da 'ya'yanta a Kano.

Malamin ya ce lamarin ya girgiza shi matuƙa har ya kasa yin barci saboda tsananin bakin ciki da damuwa.

Sheikh Daurawa ya bayyana lamarin a matsayin wani abu da ba a taɓa ganin irinsa ba ta fuskar tsananin zalunci da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng