Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Tsageru da Dama
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun nuna bajinta a ci gaba da kokarin da suke na samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
- Sojojin saman na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun yi ruwan wuta kan maboyar 'yan ta'adda a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno
- Ruwan wutar da sojojin suka yi, ta sanya an samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama tare da lalata kayayyakin aikinsu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun sake samun gagarumar nasara kan ‘yan ta’adda a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu nasarar ne bayan da suka kai wasu hare-haren sama da daddare a wasu yankunan da ke bakin ruwa a karamar hukumar Kukawa.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Borno
Dakarun sojojin sun lalata kwale-kwale, maboyar ‘yan ta’adda tare da kashe da dama daga cikinsu a yankunan bakin ruwa na karamar hukumar Kukawa da ke jihar Borno.
Majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da hare-haren ne bayan tsawon makonni na tattara sahihan bayanan sirri da yin bincike, wanda ya tabbatar da karuwar zirga-zirga da jigilar kayan aiki na ‘yan ta’adda a yankin tsibiran Malimbe–Masaram da kuma Arewacin Tumbuns.
“Bisa sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da sa ido daga sama, mun gano motsin ‘yan ta'addan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS) da ke wucewa ta Tsibirin Masaram zuwa Malimbe, tare da Toumbun Beriberi a karamar hukumar Kukawa."
- Wata majiya
'Yan ta'adda sun sha ruwan wutan Sojoji
Sun bayyana cewa an kai hare-haren ne cikin duhun dare a ranar Lahadi, 18 ga Janairun 2026, ta amfani da makamai na zamani.
“Mun kai hare-hare cikin gaggawa a jere kan wuraren da aka gano. An kashe ‘yan JAS da dama tare da lalata kwale-kwalen ruwan da suke amfani da su wajen zirga-zirga da jigilar kayayyaki a Tumbuns da hanyoyin ruwa na Tafkin Chadi."

Kara karanta wannan
Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai a Borno, mutane fiye da 40 sun mutu
“Wadanda suka rage a Malimbe da Toumbun Beriberi sun tsere nan take inda suka bar maboyarsu."
- Wata majiya

Source: Original
A cewar majiyar, bayan kammala tantance illar harin, an gano cewa ‘yan ta’addan da suka tsira sun gudu zuwa yankin Abadam cikin rudani, suna zargin cewa wasu daga cikin mutanensu na cin amanarsu ta hanyar ba jami’an tsaro bayanai.
Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi raga-raga da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Sojojin sun samu nasara bayan kai harin sama na musamman kan 'yan ta'adda a yankin Abbaga Jiri, cikin yankin Timbuktu Triangle na jihar Borno.
Nasarar ta samu ne bayan bayanan sirri daga tushe da dama da suka tabbatar da kasancewar ’yan ta’adda, gine-ginensu, da kuma wuraren ɓoye kayan aiki a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
